Ɗan Mexicon da 'Trump' ya kora daga Amurka ya kashe kansa

Guadalupe Olivas Valencia ya fado daga kan wata gada

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Guadalupe Olivas Valencia ya fado daga kan wata gada

Wani dan kasar Mexico ya kashe kansa sa'a daya bayan an fitar da shi daga Amurka.

Guadalupe Olivas Valencia, mai shekara 45, ya fado daga kan wata gada da ke kusa da kan iyakar kasashen biyu bayan an fitar da shi daga Amurka a karo na uku.

An same shi a cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai a kusa da wata jakar leda tare da wasu kayayyakinsa kuma ya mutu a asibiti jim kadan bayan hakan.

Mutumin ya mutu ne a daidai lokacin da gwamnatin Shugaba Trump ta fitar da wasu sababbin ka'idoji na korar bakin-haure daga Amurka.

Wasu ganau sun ce Mr Olivas ya yi ta ihu yana cewa ba ya son koma wa Mexico kuma da alama yana cikin matsananciyar damuwa.

Ya fado daga kan gadar ce da ke kusa da El Chaparral, babbar iyakar da ake ketara wa Amurka ta birnin San Diego daga garin Tijuana na kasar Mexico.

Kafafen watsa labaran cikin gida sun ce jakar ledar tasa ta yi kama da irin wadda jami'an shige da ficen Amurka ke zuba kayan bakin-haure a ciki.

Jami'ai a Mexico sun ce wannan ne karo na uku da aka fitar da Mr Olivas daga Amurka.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

El Chaparral babbar iyakar da ake ketarawa Amurka

Ya mutu ne sakamakon bugun zuciya.

Mr Olivas dan kabilar Sinaloa ne, daya daga cikin kabilun da ke jihohin da aka fi samun tashin hankali a Mexico, inda kuma masu safarar miyagun kwayoyi ke da karfin fada-a-ji.

'Yan kasar ta Mexico da dama na cewa suna shiga Amurka ne domin kaucewa rikice-rikicen da ake yi a kasarsu.