Turkiyya ta ɗage haramcin sa ɗan kwali ga sojoji mata

Turkish women wearing headscaves

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ƙungiyoyin addinin musulunci sun yi ta kamun ƙafa don samun ƙaruwar mata masu sanya ɗan kwali

Gwamnatin Turkiyya ta janye haramcin ɗaura ɗan kwali da ta sanya wa sojoji mata a ƙasar.

Rundunar sojan Turkiyya -- wadda tun daɗewa ake ɗauka a matsayin mai kare tsarin mulkin ƙasar wanda babu ruwansa da addini -- ita ce cibiyar ƙarshe da ta ɗage wannan haramci.

Tun a shekarar 1980 ne aka hana mata ɗaura ɗan kwali a cibiyoyin gwamnatin Turkiyya.

Sai dai shugaban ƙasar mai ra'ayin musulunci, Recep Tayyip Erdogan, ya ce haramcin, ragowar aƙidojin tauye 'yanci ne na shekarun baya.

An shafe tsawon shekaru, ana taƙaddama kan batun a Turkiyya.

Masu ra'ayin da babu ruwansa da addini na ɗaukar ɗan kwali a matsayin wata alama ta addini kuma sun zargi shugaba Erdogan da cusa manufofin musulunci, ta hanyar musuluntar da makarantun gwamnati a wani ɓangare na ƙudurin rainon "wata zuri'a mai tsoron Allah".

A cikin shekara goman da ta wuce an ɗage haramcin a makarantu da jami'o'i da ma'aikatun gwamnati sai kuma a rundunar 'yan sanda cikin watan Agustan bara.