Musulmi sun kafa asusun gyara maƙabartar Yahudawa

Jews cemetary

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

A ranar Litinin ce wasu suka lalata maƙabartar Chesed Shel Emeth a St Louis

Asusun neman gudunmawa da wasu musulmin Amurka suka kafa don gyara maƙabartar Yahudawa da aka lalata ya samu ninki huɗu na dala dubu 20 da yake nema.

Asusun da ke gangamin a "nuna wa al'ummar Yahudawan Amurka goyon baya", na da nufin taimaka wa wajen "sake gina wuri mai tsarkin".

Sama da kabari 170 aka lalata a maƙabartar Yahudawa da ke St Louis, a jihar Missouri ranar Litinin.

Lamarin ya zo ne bayan jerin barazanar nuna karan tsana ga Yahudawa.

Gangamin wanda Linda Sarsour da Tarek El-Messidi, suka ƙaddamar ya karɓi gudunmawa fiye da 3,000 ta sama da dala dubu 85.

Bayanan hoto,

An kakkarya gine-ginen da ake alamta kaburbura da su a cikin maƙabartar

Shafin tara gudunmawar ya ce " Musulmin Amurka na tare da al'ummar Yahudawan Amurka wajen yin Allah wadai kan wannan mummunan aikin saɓo."

Asusun wanda har yanzu yake karɓar gudunmawa, na da niyyar gyara ɓarnar da aka yi a maƙabartar Chesed Shel Emeth ta St Louis, amma dai masu gangamin sun ce duk ƙarin gudunmawar da aka samu za a yi amfani da shi ne wajen "tallafa wa sauran cibiyoyin Yahudawa da aka lalata a faɗin ƙAsar".

A ranar Talata, ƙungiyoyin musulmi na Islamic Society of North America (ISNA) da majalisar bunƙasa alaƙa tsakanin Amurka da muslumi shiyyar Missouri suka yi tir da lalata kaburburan Yahudawa.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyanar barazanar da ake yi wa al'ummar Yahudawa a baya-bayan nan cikin ƙasar a matsayin wani "abin tsoro da ke da ciwo matuƙa".

Sai dai wata cibiya mai rajin bunƙasa kare mutuncin juna ta Anne Frank ta bayyana kalaman Trump a matsayin "wani mummunan ɗan ba wajen nuna fifiko".

Sakataren yaɗa labarai a fadar White House Sean Spicer ya ce ba haka abin yake ba, ya dage a kan cewa shugabansa "yakan yi tir cikin amo mai ƙarfi" a kan duk wani nau'in wariyar launin fata da kuma mutanen da ba su da jimirin wasu masu bambancin ra'ayi.