Trump ya soke kariyar da ake bai wa masu sauya jinsi

White House

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Kimanin masu zanga-zanga 200 suka hallara a White House domin nuna rashin jin dadinsu da matakin Mista Trump

Gwamnatin Donald Trump ta soke kariyar da Amurka ke bai wa daliban da suka sauya jinsinsu na ainihi.

Wannan kariya dai na bai wa daliban damar yin amfani da ban dakunan makaranta daidai da jinsin da suka zaba.

Ma'aikatar shari'ah da ta ilmi a Amurka sun ce tsare-tsaren da aka bijiro da su bara a karkashin gwamnatin Barack Obama sun kawo rudani don haka ana bitarsu.

Matakin dai ba zai shafi tsare-tsaren hana cin zali ba.

Daya daga cikin mutanen da ke kare masu sauya jinsi a Amurka, Ames Simmons, ya ce tsare-tsaren sun zama wajibi da nufin kare dalibai daga fuskantar wariya.

Ya ce, "Mun yi imani cewa wannan, wani mummunan sako ne yau gwamnatin Trump ke isar wa ga wasu matasa masu rauni a kasarmu."

Tsohon Shugaban Amurka, Barack Obama, ne ya ba da umurnin ga makarantun kasar, inda masu rajin kare hakkin masu sauya jinsi suka yabe shi a kan hakan.

Amma masu sukar lamiri sun ce hakan barazana ce ga sauran daliban, kuma kamata ya yi a bar jihohi su yi dokar ba wai ta zama ta kasa baki daya ba.

Dokar dai ta janyo cece-kuce inda har sai da aka shigar da kararrakin kalubalantarta a jihohi 13.

A ranar Laraba ne gwamnatin shugaba Donald Trump ta tura sakon soke dokar makarantu, inda ya ce dokar ta haddasa rudani.

Ba lallai sabon matakin Mista Trump din ya yi wani tasiri na a-zo-a-gani-ba saboda dama tuni wata kotu a jihar Texas ta dakatar da amfani da dokar na wucin-gadi a watan Agustan bara.

A bara ne bangarorin shari'a da na ilimi suka bai wa makarantun gwamnati damar barin masu sauya jinsi su yi amfani da duk ban dakin da suka zaba na maza ko mata.