Fasinja na rububin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna

Jirgin kasan kan shafe sa'o'i biyu daga Abuja zuwa Kaduna
"Amfanin jirgin nan yana da yawa, musamman ma ta fannin tsaro da farashi mai rahusa, ga shi kuma yana rage gajiyar hanya," in ji Lauya Ummu Abubakar Daba, wata fasinja da ta hau jirgin kasa na zamani da ke jigila daga Abuja zuwa Kaduna.
Wakilin BBC Ibrahim Isa, wanda ya yi bulaguro da jirgin daga Abuja zuwa Kaduna don ganin yadda yake shafar rayuwar jama`a, ya ce jirgin na ci gaba da samun karbuwa a wajen al`umar kasar, kama daga masu ido-da-kwalli zuwa marasa galihu, ciki har manyan jami`an gwamnati da `yan kasuwa.
Jirgin dai ya fara ne da jigilar jama`a kyauta sau daya a rana, amma yanzu yana kaiwa da komawa daga Abuja zuwa Kaduna sai uku a rana, kuma farashin tikitin jirgin kan kama daga naira dari shida zuwa naira dari tara.
Taragun jirgin hudu ne, daya na masu sukuni ko `yan kasuwa, ragowar uku kuma ta sauran jama`a, sannan an kayata su da na`urar sanyaya daki, ga kuma makewayi.
Batun tsaro na daga cikin abubuwan da ke kara wa jirgin tagomashi, musamman ma matsalar fashi da satar mutune da ake fama da ita a kan hanyar motar Abuja zuwa Kaduna, duk kuwa da cewa mahukunta na ikirarin daukar matakan murkushe miyagun da ke aika-aika a kan hanyar da kuma dazukan kewaye.
Fasinjoji da dama sun shaida wa BBC cewa jirgin yana taimakawa wajen rage cinkoso a kan hanyar mota ga kuma rangwamen farashi.
Wani fasinja da iyalinsa cewa ya yi "tashar jirgin kadai abin sha`awa ce. Abu ne da muke gani a kasashen da suka ci gaba, yanzu ya iso kasarmu."
Wasu fasinjoji sun nuna farin cikinsu game da samar da jirgin
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
Sakamakon ribibin da jama`a ke yi suna shiga jirgin, kujeru 320 da aka tanada na neman yi wa fasinjoji kadan, kuma wannan ne ya sa Zainab Buba Galadima, wata fasinja ke cewa akwai bukatar gyara.
Ta ce "akwai rangwame, amma korafina shi ne suna sayar da tikiti fiye da adadin kujerun jirgin. Za ka ga mutane da dama na tsaye ko zaune a kasa. Akwai masu goyo, akwai tsofaffi. Ya kamata a samar da karin taragogi ta yanda kowa da kowa zai samu wajen zama.
Kamfanin Sinawa mai suna China Civil and Engineering Construction Company ne ya yi kwangilar gina hanyar jirgin, a kan dala $874m.
Bankin bunkasa cinikin China, wato China Exim Bank ne ya ba da rancen dala miliyon 500 daga cikin kudin, yayin da gwamnatin Najeriya ta biya ragowar.
Kuma a halin da ake ciki, Sinawa kwararru ne ke aiki tare da ma`aikatan jirgin kasan Najeriya wajen yin jigila da jirgin da fatan cewa za a su sakam ma `yan Najeriya ragama nan da shekaru biyar masu zuwa.
Jirgin na tafiyar kilomita 100 a cikin sa`a guda, kuma yana da kananan tasoshi goma daga Idu zuwa Rigasa. Kuma tashar Rigasa ce zangon karshe ga masu zuwa birnin Kaduna
Tashar Rigasa ce zangon karshe ga masu zuwa Kaduna
Sai dai a cikin wata shida da jirgin ya kwashe yana jigila, ya lalace har sau biyu, lamarin da ya haddasa jinkirin jigilar fasinjoji tare da jefa su cikin kunci, har ta kai ga wasu na ganin cewa da wuya jirgin ya dore idan aka danka wa `yan Najeriya linzami.
Amma Manajan Jirgin kasan Abuja-Kaduna, Mista Paschal Nnorli ya ce za su magance matsalar ba da jimawa ba, yana jaddada cewa " kawunan jirgi biyun da muke amfani da su, da su aka yi amfani wajen gina layin dogon.
Kuma kasancewar an dade ana amfani da su, sun fara gajiya. Wannan na daga cikin dalilan da suka sa jirgin lalacewa har sau biyu. Kuma nan ba da da jimawa ba za a magance wannan matsala da zarar sabbin kan jirgin da muka yi oda sun iso."
Baya ga dimbin matasan da suka samu aiki a hukumar jirgin kasan, sauran jama`a a bangare guda, jama`a da dama na samun rufin asiri a kasuwanni da tasoshin motar da akan kafa a gefen tasoshin jirgin kasan.
Wani Direba a Rigasa ya shaida wa BBC cewa "idan wannan jirgi ya kawo mutane mukan dauka zuwa kasuwa da Kano-road da Kawo har Kano ma har Zaria duk ana dauka, kuma muna samun rufin asiri."
Wasu 'yan kasar na yabawa gwamnati suna masu cewa motsi ya fi labewa
Ba dukan `yan Najeriya ne dai ke zumudin nasarar da kasar ta samu wajen kaddamar da jirgin kasa na zamanin ba, kasancewar wasu na da ra`ayin cewa ya kamata a ce kasar ta dade ta cimma hakan, bisa la`akari da cewa ta gaji layin dogo na gargajiya mai tsawon kilomita 3,505km daga Turawan mulkin mallaka.
Amma wasu `yan kasar kuma na ganin cewa hobbasar da mahukuntan Najeriyar suka yi sai sambarka, kasancewar motsi ya fi labewa!