Leicester City ta kori kocinta Claudio Ranieri

Ranieri

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A watan Yulin 2015 aka nada Ranieri kocin Leicester City

Leicester City, ta kori kocinta Claudio Ranieri wata tara bayan ya jagorance ta ta dauki kofin Premier na farko a tarihinta.

Maki daya ne tsakanin kungiyar da rukunin faduwa daga gasar ta Premier, yayin da ya rage wasanni 13 a kammala gasar ta bana.

A sanarwar da ta fitar ta sallamar kocin, ta bayyana cewa hukumar kungiyar ta dauki wannan matakin ne duk da cewa abu ne mai ciwo, amma ya zama dole domin amfanin kungiyar.

Ranieri, mai shekara 65, ya jagoranci kungiyar ta dauki kofin na Premier a bara duk da cewa kusan ba wanda ya taba tsammanin hakan za ta kasance a farkon gasar ta bara.

Sai dai Sanarwar ta jaddada cewa matsayin kocin na mai horad da 'yan wasanta da ya fi kowa nasara, abu ne da ba tantantama a kansa.

Leicester ta dauki kofin ne da tazarar maki 10, amma kuma a bana wasa biyar kawai ta ci a gasar, ya zuwa, kuma za ta iya kasancewa mai rike da kofi ta farko da ta fadi dag gasar tun 1938.

Kungiyar ta yi rashin nasara a wasanninta biyar na karshen nan na Premier, kuma ita kadai ce daga cikin kungiyoyin da ke manyan gasar lig-lig hudu na Ingila da ba ta ci kwallo ba a gasarta a shekarar nan ta 2017.

A farkon watan nan ne kungiyar ta bayyana cewa tana goyon bayan kocin dan Italiya ba tare da wani shakku ba.