An ɗaure wani malamin Yahudu kan tauye hukuncin addini

Asalin hoton, AFP
An kuma zarge shi da yin dumu-dumu cikin kuɗaɗen gudunmawar agaji
An ɗaure wani tsohon babban malamin Yahudawa sama da shekara huɗu a gidan yarin Isra'ila bayan an caje shi kan zarge-zargen cin hanci.
Malamin Yona Metzger ya amsa cewa ya karɓi sama da dala miliyan ɗaya a matsayin cin hanci.
An kuma zarge shi da yin dumu-dumu cikin kuɗaɗen gudunmawar agaji da ake tarawa.
Ya kuma karɓi wasu kuɗi da aka ba shi don jirkita hukuncinsa a kan wasu harkokin addini.
A shekara ta 2013, an yi wa Yona Metzger ɗaurin talala bisa zargin aikata cin hanci kafin muhimmin wa'adinsa a matsayin babban malamin Yahudawa ya zo ƙarshe.