Wasu 'yan bindiga sun kashe sojan jamhuriyar Nijar 15

Mouhammadou Issoufou

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaban jamhuriyar Nijar Mouhammadou Issoufou na yunkurin kafa wata rundunar soja ta musammam da hadin gwiwar sauran kasashen Sahel don yaki da ta'addanci

Jami'an tsaro a Nijar sun ce an kashe soja goma sha biyar a wani harin da ake zargin masu da'awar musulunci ne suka kai kan ayarin masu sintiri a kusa da kan iyaka da kasar Mali.

Wasu mutane ne dauke da makamai suka kai wa sojojin hari yayin da suke sintiri a yankin Walam cikin jihar Tilabery.

Wani mai magana da yawun jami'an tsaro a kasar kanal Abdul ya ce an kuma jikkata soja goma sha tara.

Ya ce sojoji sun kaddamar da wani yunkuri don gano maharan. Jamhuriyar Nijar na daya daga cikin kasa biyar da suka amince a farkon wannan wata su kafa wasu dakarun hadin gwiwa don yaki da ta'addanci a yankin Sahel.

Yarjejeniyar ta biyo bayan wani harin da masu ikirarin jihadi suka kai Mali cikin watan jiya, wanda ya yi sanadin mutuwar kimanin mutum tamanin.