Shugaba Trump ya ce sai sun maƙare rumbunsu na nukiliya

Wani mutum-mutumin makamin nukiliyar Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wani mutum-mutumin makamin nukiliyar Amurka

A jawabinsa na farko kan makaman nukiliya tun bayan hawansa kan karagar mulki, Donald Trump ya ce Amurka na son faɗaɗa rumbunta na nukiliya.

Mr. Trump ya ce ya gwammace wanzuwar duniya ba tare da makamin nukiliya ba, amma Amurka ba za ta sakankance ta zama kurar baya wajen yawan nukiliya ba, don haka yana son su "maƙare rumbu."

Shugaba Trump ya ce yarjejeniyar taƙaita yaɗuwar nukiliya da Amurka ta sanya hannu da Rasha wadda ta ce kamata ya yi ƙasashen su mallaki adadin makaman nukiliya daidai-wa-daida, raguwar dabara ce.

Game da gwaje-gwajen makami mai linzami da Koriya ta arewa ke yi, Donald Trump ya ce Idan China ta so tana iya makure mahukuntan birnin Pyongyang cikin sauki.

A cewar wata ƙungiya mai rajin taƙaita yaɗuwar makamai ta Amurka, ƙasar tana da makaman nukiliya guda 7,100 a lokaci guda kuma Rasha tana da 7,300.

A lokacin yaƙin neman zaɓensa, Mr Trump ya yi kira ga Amurka ta ƙara adadin nukiliyar da ta mallaka bayan shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce ƙasarsa na buƙatar bunƙasa ƙarfin rundunar sojanta ta fuskar makaman nukiliya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Donald Trump na son Amurka ta sha gaban kowacce ƙasa a duniya ta fuskar yawan makaman nukiliya