Nigeria: Daurawa ya soki dokar hana kara aure ta Kano

Sarki Sunusi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sarki Sunusi ya ce mutane na auren mata su haifi yara da yawa su kasa ba su tarbiyya

Malaman addinin Musulunci a jihar Kano suna ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan matakin kafa dokar da za ta hana marasa hali auren mace fiye da daya a jihar.

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ne, ya nemi bullo da wannan doka da kuma karin wasu matakai, da niyyar magance dumbin matsalolin da suka dabaibaye harkar auratayya a kasar Hausa.

Sai dai a wata hira da ya yi da BBC, shugaban hukumar Hizbah ta jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, na ganin wayar da kai ne kawai zai magance matsalolin aure, amma ba wata doka ba.

Ya ce, "Dama ita maganar aure fiye da mace daya Allah ya riga ya sa sharadi a Al-kur'ani sai in mutum zai iya adaci, kuma malamai suna karawa da wasu sharudda 13 da dole mutumin da ke son kara aure ya cika su.

Kenan kamata ya yi a ce wadannan sharuddan ne za a wayar wa da mutane kai a kansu. A sanar da mai son kara auren da wacce za a aura, da dalilin kara auren don su san sharuddan."

Sheikh Daurawa ya kara da cewa matsalolin aure sun ta'allaka ne a kan rashin ilimin su ma'auratan a kan ma'anar auren kansa.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ya ce "Akwai wanda aure ya wajaba a kansu, da wadanda ya haramta a gare su, akwai wadanda an so su yi auren, akwai kuma wanda ba a so su yi auren ba, don haka ya zama wajibi a wayarwa da kowa kai don sanin matakin da ya fada kafin akai ga yin doka."

Malamin ya yi kira ga masarautar Kano da ma gwamnatin jihar da cewa, kamata ya yi a saka batun aure a cikin tsarin karatun makarantu tun daga sakandare.

"Hakan zai sa tun kafin mutum ya kai munzalin auren ya san dalilan da suka sa ake yi da kuma sharuddansa, amma idan aka yi doka ba tare da an ilimantar da mutum akan sharadin dokar ba, to dokar ma ba za ta yi aiki ba."

Sai dai a hannu guda kuma Shehin Malamin ya koka kan yadda ake yawan sakin aure da yadda zawarawa ke karuwa, yana mai cewa wayar da kai ne zai rage faruwar hakan.

"Abin takaicin shi ne yadda za ka ga wasu mazan suna da halin rike mata har hudu ma, amma sai matarsu ta cikin gida ta ja daga ta hana su yin hakan, to su ma ya kamata a yi doka da za ta ba su karfin gwiwa su dinga yin auren," Inji Malam Daurawa.

Me ya sa dokar ba za ta yi aiki ba?

Sheikh Daurawa ya ce babban kalubalen da ke tattare da wannan doka shi ne, ta yadda za a gane wanda ke son kara auren yana da hali ko ba shi da hali.

Bayanan hoto,

Sheikh Daurawa ya ce ya ga talakan da ya sayar da rigarsa don ciyar da matarsa

Na biyu kuma zai yi wahala a yi binciken har a gano gaskiyar lamarin, "Mai kudi ya sha yin aure fiye da daya ya samu karayar arziki daga baya, haka ma talaka yana iya aure da yawa daga baya ya yi arziki, to ta ya ya za a aiwatar da dokar a irin wannan yanayi," a cewarsa.

Ga karin bayanin Malamin:

Bayanan sauti

Daurawa ya yi tsokaci kan dokar hana kara aure

A ganinsa ilimantar da mutane sosai a kan dokokin shari'a da sharuddan Allah a kan batun aure ne kawai hanyar da za a bi don magance matsalolin da suka dabaibaye al'umma.

Ya ce a wasu lokutan ma halin rike aure ba a arziki ko wadata yake ba, ya danganta da irin zuciyar mutum ne ta yin abubuwa.

Wannan batu dai ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a tsakanin al'ummar Najeriya ba ma jihar Kano ba kawai, inda mutane da dama suka yi ta tofa albarkancin bakinsu a shafukan sada zumunta da muhawara.

Sai dai dama dokar ta sarki Sunusi ba ta riga ta fara aiki ba tukun, don sai an mika ta ga kwamitin malamai sun duba dacewarta ko akasin hakan kafin daga bisani a mika ta ga majalisar dokokin jihar don tabbatar da ita.