Wanne tasiri shafukan sada zumunta ke yi a rayuwarku?

Abdulganiyyu Rufai Yakubu, shugaban Digital Development Hub, Abuja
Bayanan hoto,

Abdulganiyyu Rufai Yakubu ya ce harkar sadarwa ta zamani "sha-kundum" ce

A ranar Litinin ne aka bude wani babban taro a kan kafofin sadarwa na zamani, wato social media, a Legas, babban birnin kasuwancin Najeriya.

Taron dai kan tattaro masana, da masu fafutuka, da masu kirkira, da ma 'yan kasuwa, don su tattauna sabbin tunani da ci gaban fasaha da yadda za a iya amfani da su don saukaka rayuwar dan-Adam.

Wannan ne dai karo na biyar da ake gudanar da taron, wanda masu shirya shi suka ce yakan samu halartar mutane fiye da 12,000 duk shekara.

A bana dai za a gudanar da kananan taruka 122 a karkashin babban taron, wadanda za su tattauna batutuwa da dama da suka hada da hanyoyin samun kudi ko sana'a a kafofin sadarwa na zamani, da makomar kafofin yada labarai na "gargajiya" yayin da suke fuskantar kalubale daga kafofin sadarwa na zamani, da sauransu.

BBC ma za ta karbi bakuncin wani karamin taro inda za a tattauna a kan yadda mata za su taka rawa su kuma yi fice a kafofin sadarwa na zamani.

Hanyar samun kudi

Dangane da hanyoyin samun kudi a kafofin sadarwa na zamani da ma intanet baki daya dai, wani matashi da ke shugabantar wata cibiya mai kyankyasar kananan sana'o'i a intanet ya kwatanta su da "sha-kundum".

A cewar Abdulganiyyu Rufa'i Yakubu, "Kimiyyar fasahar sadarwa wani fage ne wanda yake a bude, kuma wanda yake sha-kundum".

Ya kuma ce, "Kudin da ke cikin wannan harka a bayyane yake. Har kullum ana cikin yunwa da kishirwar manhajojin magance matsaloli ta hanyar fasahar sadarwa; {akwai wani bangare na wannan harka wanda shi} kadai ya isa ya magance dukkan matsalar rashin aikin-yi a manya-manyan birane na Afirka".

Bayanan hoto,

Muhammad Ibrahim Jega ya yi kira ga matasa su daina bata lokaci akafofin sadarwa na zamani

Muhammad Ibrahim Jega na daga cikin kwararru a wannan fanni, kuma shi ne ya kirkiri wata kungiya da ke wayar da kan matasan arewacin Najeriya game da amfanin da ake samu a kafofin sadarwa na zamani, wato Startup Arewa.

Ya shaida wa BBC cewa, "Mun gane yaranmu suna zuwa intanet su yi ta batsa suna zagin gwamnati, {abin} da ba {zai} kara musu komai ba. Wani na nan shi a intanet din da kuke zuwa kuna bata lokacinku, ko wanne minti daya kudi yake samu".

Bayanan bidiyo,

Garabasar da ke tattare da kafafen sadarwa na zamani

'Rumfar BBC'

Karamin taron da BBC za ta karbi bakuncinsa zai duba irin damar da mata ke da ita da kalubalen da suke fuskanta a wannan harka ta kafofin sadarwa na zamani.

Wadannan dama da kalubale sun shafi daukar su aiki da ma yi musu karin girma a harkar fasahar zamani a Afirka, tun ma daga matakin ilimi ko karatun boko.

Bayanan hoto,

Wakiliyar BBC Anne Soy za ta fadi irin gwagwarmayar da ta sha

Duk da ci gaban da aka samu a 'yan shekarun nan dai, har yanzu mata tsiraru ne a sana'o'i da dama ciki har da aikin jarida.

Daya daga cikin fitattun wakilan BBC a Afirka, Anne Soy, za ta gabatar da jawabi a kan irin abubuwan da ta fuskanta da nufin bai wa mata damar fahimtar yadda za su yi fice a harkar sadarwa ta zamani da aikin jarida.

Mako guda za a shafe ana tattauna batutuwa daban-daban a wurin wannan taro, kuma za ku iya samun cikakkun rahotanni a BBCHAUSA.COM.