Mata masu bin maza kaɗai ba su cika more wa jima'i ba

Sex

Asalin hoton, Thinkstock

Wani bincike ya nuna cewa mata bi-maza suna da ƙarancin fitar da maniyyi ko kuma inzali, idan an kwatanta su da maza ko kuma 'yan maɗigo ko kuma mata masu bin maza da mata.

Binciken ya zo ne sakamakon wani nazari da aka yi a kan mutum dubu 52 da 600 a Amurka, don zaƙulo "giɓin inzali" a tsakanin jinsi da kuma mutane masu bambancin sha'awar saduwa.

Rahoton wanda aka buga a mujallar in Archives of Sexual Behaviour ya bankaɗo "mabambantan ɗabi'u da abokan zama za su gwada don ƙara samun yawan inzali".

Ɗabi'un sun haɗar da jima'in baki da shasshafa al'aura.

Nazarin na Jami'ar Indiana da Jami'ar Chapman da Jami'ar Claremont Graduate, ya nuna rabe-raben mutanen da akasari ke samun inzali a kan:

 • 65% Mata bi- maza
 • 66% Mata bi- mata-maza
 • 86% Mata 'yan maɗigo
 • 88% Maza bi- mata-maza
 • 89% Maza 'yan luwaɗi
 • 95% Maza bi-mata

Ayarin masu binciken ya ce: "Nazarin, sai dai, ya nuna cewa ana iya rage wannan giɓi na inzali.

Sauran ɗabi'u

Rahoton ya ce mata bi- maza ƙalilan ne suke kai wa ƙololuwar jin daɗi sakamakon saduwar turmi da taɓarya kaɗai.

Nazarin ya nuna "matuƙar muhimmancin haɗawa da jima'in baki da sauran wasu abubuwa a yayin saduwa".

Akwai wata siga ƙarara tsakanin yawan jima'in baki da yawan inzali a wajen mata bi-maza, da mata masu maɗigo da mata bi-mata-maza da maza 'yan luwaɗi da maza bi- mata-maza.

A wajen maza bi- mata ne kawai ba a iya gano hakan ba.

Wasu ɗabi'u masu alaƙa da ƙaruwar inzali a wajen mata su ne:

 • Tambayar abin da suke so yayin kwanciya
 • Kwarzanta abokan zamansu kan abin da suka yi yayin kwanciya
 • Tsokanarsu ta hanyar wata batsa
 • Sanya kayan barci masu motsa sha'awa
 • Gwada sabbin sigogin kwanciya
 • Saduwa ta dubura
 • Kalamai da kwatanta ƙawa-zucin batsa
 • Maganganun batsa da furucin soyayya a yayin jima'i

Marubutan wannan rahoto sun ce akwai wasu azanci na zamantakewa da na salsalar rayuwa a kan dalilan da suka sa maza da mata ke da bambancin inzali.

Misali akwai tsangwama da ake nuna wa matan da ke bayyana sha'awar jima'i, abin da ke daƙile gano sabbin hanyoyin more rayuwar kwanciya da kuma imanin da wasu maza suka yi cewa akasarin mata suna kawowa ne kaɗai idan an yi saduwar turmi da taɓarya.

Kuma daga fahimtar tsarin salsalar rayuwa inzalin mace da namiji suna da manufofi iri daban-daban waɗanda kuma ke da wani tasiri.

Inzalin namji bai wuce kawowar da yake yi don samun ƙaruwa ba, yayin da kuma na mace "ƙara shaƙuwa yake sanya wa da daɗaɗɗen abokin zama", in ji rahoton.