BBC ba ta ji daɗin yi wa 'yan jaridanta leƙen asiri ba

BND

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

BND na da wata babbar tashar sauraron bayanai a yankin Bad Aibling kusa da birnin Munich

BBC ta bayyana rashin jin daɗinta kan zargin leƙen asirin da hukumar Jamus ke yi wa 'yan jaridar ƙasashen waje ciki har da na BBC.

Hukumar leƙen asiri ta Jamus BND ta riƙa satar sauraron wayoyin salula da saƙwannin i-mail da na fas, ciki har da lambobin BBC fiye da goma a London da Afghanistan, a cewar kafar yaɗa labaran intanet ta Spiegel.

Kafar yaɗa labaran ta Jamus ta yi zargin cewa leƙen asirin, wanda aka fara tun cikin 1999, ya kuma shafi kamfanin dillancin labarai na Reuters da jaridar New York Times.

Mai magana da yawun BBC ya ce "Ranmu ya ɓaci da jin waɗannan bayanai."

"Burin BBC shi ne ta bayar da sahihan labarai da bayanai ga mutane a faɗin duniya, kuma kamata ya yi 'yan jaridarmu su samu damar yin aiki cikin 'yanci da aminci, da cikakkiyar kariya ga majiyoyinsu. Muna kira ga dukkan gwamnatoci su mutunta aikin jarida cikin 'yanci."

BBC dai ta tunkari hukumar BND game da zarge-zargen, amma dai ya zuwa yanzu ba ta samu amsa ba.

Spiegel ta ruwaito cewa aƙalla lambar waya 50 na 'yan jaridar ƙasashen duniya ne BND ke bibiya.

Kafar yaɗa labaran Jamus din wadda ake mutuntawa tana shirin fitar da ƙarin bayanai game da zargin leƙen asirin ranar Asabar.

Kafar labaran ta ga wasu takardu na wani bincike da majalisar dokokin Jamus (Bundestag) ke yi game da rawar da BND ta taka a wani gagarumin leƙen asiri da Amurka ta jagoranta.

Ba'amurke mai kwarmata bayanai Edward Snowden ya fallasa wani shirin leƙen asirin da ya karaɗe duniya wanda hukumar tsaro ta Amurka (NSA) ta yi da taimakon BND da kuma wata hukumar leƙen asirin Burtaniya GCHQ.