Wasu sun hau maleji a jirgin sama zuwa Saudiyya

Pakistan Airlines overboarded with passengers
Bayanan hoto,

A baya-bayan nan kamfanin jiragen saman Pakistan na fama da zubewar ƙima

Kamfanin jiragen sama na Pakistan yana bincike kan yadda aka bar ƙarin fasinja bakwai suka yi maleji tsaitsaye cikin wani jirgi zuwa ƙasar Saudiyya.

Wani mai magana da yawun kamfanin ya faɗa wa BBC cewa a ranar 20 ga watan jiya ne aka bar fasinjojin suka yi maleji daga Karachi har zuwa Madina, duk da yake kujerun jirgin sun cika.

Wata jaridar Pakistan Dawn ce ta fara bankaɗo bayanan wannan al'amari na maleji a jirgin sama.

Ta ruwaito cewa ma'aikatan kamfanin jirgin sun ba da ƙarin takardun hawa jirgi da aka rubuta da biro.

Jaridar ta kuma ambato kaftin ɗin jirgin, Anwer Adil na dagewa a kan shi lallai bai san da labarin ƙarin fasinjojin ba, har sai da suka ɗaga.

Ƙwararru kan sufurin jirgin sama sun ce irin wannan cunkusa mutane a jirgi, ka iya janyo matsaloli, idan buƙatar kwashe fasinjojin cikinsa ta taso da gaggawa.