An hana wasu kafafen watsa labarai shiga taron Trump

Sean Spicer

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Spicer ya ce ba za su bar 'yan jarida su ci gaba da bata musu suna ba

Fadar White House ta hana wasu manyan kafafen watsa labarai shiga wurin wani taro da Shugaba Trump ya yi.

An hana BBC da CNN da the New York Times da kuma wasu manyan kafafen watsa labarai daga shiga wurin jawabin da kakakin fadar ta White House Sean Spicer ya hada ba tare da gaya musu dalilin yin hakan ba.

Sai dai an bar kafafen watsa labarai irin su ABC, Fox news, Breitbart news da the Washington Times suka halarci taron manema labaran.

Lamarin ya faru ne sa'o'i da dama bayan Shugaba Donald Trump ya sake yin kakkausan suka ga kafofin watsa labarai, yana mai cewa masu watsa "labaran kanzon-kurege" "makiyan Amurkawa" ne.

A baya dai Mr Trump ya ware CNN da the New York Times inda ya yi ta caccakar su.

Shugaba Trump bai ji dadin wasu rahotanni na baya bayan nan da suka yi ikirarin cewa jami'an yakin neman zabensa sun rika yin mu'amala da jami'an leken asirin Rasha.

A caccakar da ya kwashe minti 15 yana yi wa 'yan jarida, ya ce bai kamata a bar su su rika amfani da majiyoyi a cikin labaransu ba, ba tare da ambato ko su waye majiyoyin ba.

Har yanzu fadar White House ba ta fadi dalilan da suka sanya aka hana kafafen watsa labaran shiga wurin taron ba.