Shin akwai yiwuwar samun dan wasa kamar Messi a Nigeria?

Pupils at FCBescola Lagos in Nigeria

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona na shirin kaddamar da kwalejin horarwa ta kwallon kafa a Legas, birni mafi girma kuma cibiyar kasuwancin Najeriya.

Kwalejin wadda za ta zama irinta ta farko a nahiyar Afirka, za a tafiyar da ita bisa tsarin babbar kwalejin kungiyar ta 'La Masia Academy' da ke kasar Sifaniya.

Ita dai wannan babbar kwalejin ta samar da fitattun 'yan wasa kamar Andres Iniesta da Lionel Messi da kuma Xavi.

Sabuwar kwalejin ta Najeriya da aka yi wa lakabi da 'FCBEscola Lagos', za ta zauna ne na wicin-gadi a filin wasa na Teslim Balogun da ke unguwar Surulere, a birnin na Legas.

Abun da za ka fara hange da ka shiga kwalejin shi ne katafaren hoton dan wasan kungiyar na tsakiya wato Iniesta.

Sannan kuma an sanya hotunan fitattun 'yan wasan kungiyar kamar Lionel Messi da Luis Suarez da kuma Neymar, a kan allunan tallace-tallace.

Imalashe Sulyman

"Kwallon kafa ba wasan yara kanana ba ne....ni ma ina son na zama 'yar kwallon da ta shahara kuma ina son zama kamar Messi"

Ana horar da kananan yara masu shekara biyar zuwa 18, yadda tamaula take a mahangar kungiyar Barcelona.

Yanzu haka akwai yaran da suke biya domin samun horaswa kamar guda 400, a inda suke biyan $600, a kowace shekara.

Suna daukar darasi kamar sau daya a mako.

Kuma kusan za a iya cewa burin kowane daya daga cikin daliban bai wuce samun damar zuwa babbar kwalejin Barcelona ta 'La Masia Academy' da ke kasar Sifaniya.

Yadda dalibai ke aiki tare

Daga cikin daliban wannan kwaleji akwai Imalashe Sulyman daga Yaba ta Legas.

Kuma Imalashe na daya daga cikin 'yan mata uku da ke wannan kwaleji.

"Ina matukar son zama a nan saboda akwai nuna abokantaka sannan kuma za ka ji annashuwa idan kana buga leda a nan," In ji Imalashe.

Asalin hoton, Jasper Juinen/Getty

Bayanan hoto,

Dan wasan Barcelona kuma dan kasar Argentina, Lionel Messi na daya daga cikin fitattun 'yan wasa a duniya

Bayanan hoto,

The school aims to nurture young talent to become future stars

Yanzu haka dai Barcelona ce kawai daga cikin manyan kungiyoyin kwallo a duniya ta kafa irin wannan kwaleji a nahiyar Afirka. Kuma wwalejin na samun karbuwa daga ciki da wajen Najeriya.

Bayanan hoto,

Somagbe Ipedumi na da burin zama kamar Messi da Neymar

Somagbe Ipedumi, daga Ikorodu da ke birnin Legas, ya fadi cewa dan wasan Barcelona kuma dan kasar Brazil wato Neymar ne dan wasan da ya fi kauna kuma yana son ganin ya zama kamarsa.

"A koyaushe ina da burin taka leda a Barcelona saboda haka babbar dama ce mutum ya kasance a nan," In ji shi.

"Wasa a nan wurin ba karfi ba ne, illa dai yin aiki tare da abokan wasanka, ina tunanin daga nan zan je wuraren da ban ma zata ba."

Wannan kwalejin da ke a birnin Legas wata dama ce ga Barcelona ta amfana daga irin basirar da Allah ya huwace wa 'yan Najeriya miliyan 170.

Bernat Gorriz, kociyan Kwalejin Horarwa a kwallon kafa ta Barcelona da ke Legas.

Shi ma kocin kwalejin, Bernat Gorriz, ya ce za a iya samun 'yan kwallo masu hazaka nan gaba, a Najeriya.

"Wani babban abu mai mahimmanci da al'ummar Afirka take da shi, shi ne yanayin jikinsu saboda haka idan za su fahimci yadda muke taka leda, ina mai tabbatar maka za mu samu 'yan wasa masu kyau a Najeriya."

Da aka tambaye shi ko za a samu irin Lionel Messi nan gaba daga Najeriya, sai ya ce: "Ban sani ba ko za mu sake samun wani dan wasa kamar Messi amma dai tabbas za mu horas da yaran nan yadda za su yi su zama kamar Messi"