Akwai 'yan Boko Haram a shugabannin Borno - Janar Irabor

Dakarun Najeriya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kakkabe Boko Haram daga dajin Sambisa

Kwamandan rundunar Zaman Lafiya Dole mai yaki da Boko Haram ya ce rundunar ta samu nasarar cafke wasu shugabannin al'umma a jihar Borno bisa zargin hannu a kungiyar ta Boko Haram.

Manjo Janar Lucky Iraboh ya ce kawo yanzu rundunar ta kama da dama daga cikin shugabannin da suka hada da wani shugaban wata karamar hukuma a jihar.

Mista Irabor ya kara da cewa wasu daga cikin shugabannin suna da alaka da kungiyar ta Boko Haram, a inda wasu kuma su ne ma suka kirkire ta.

Ga dai yadda hirarsa ta kasance da wakilin BBC, Chris Ewokor, yayin wata ziyarar gani da ido da ayarin na BBC ya kai jihar ta Borno a baya-bayan nan.

Bayanan sauti

Janar Irabor ya ce Allah ne kawai ya san lokacin da rikicin BH zai kare