Syria: Bama-bamai sun kashe dimbin mutane

Syria Conflict Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gidan telibijin na Syria ya nuna hoton inda lamarin ya faru

'Yan kunar bakin wake sun kai hare-hare da bama-bamai a wasu gine-gine biyu na jami'an tsaro na gwamnatin Syria a birnin Homs.

An kashe mutane masu yawan gaske ciki har da wani shugaban tattara bayanan sirri na soji a yankin.

Wasu rahotanni na cewa mutane arba'in aka kashe wasu da dama kuma suka jikkata. Kungiyar Tahrir al-Sham, wadda gamayyar kungiyoyin 'yan-tawaye ce dake karkashin jagorancin wani tsohon reshe na kungiyar al-Qaeda, ta ce 'yan kunar bakin wake biyar ne suka kai hare-haren.

Shaidu sun ce ko baya ga tashin bama-bamai, wasu daga cikin maharan sun kuma yi amfani da bindigogi wajen kashe mutane.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Syrian Observatory for Human Rights ta ce an kai hare-haren ne a hedikwatar soji da kuma ofishin 'yan-sandan ciki dake unguwannin Ghouta da Mahatta, wadanda ake jin suna da cikakken tsaro.

A wani mataki mai kama da martani kuma, jiragen saman yaki na soja sun kai hare-hare a yankin da ya rage a hannun 'yan-adawa a birnin, ko da ya ke dai ba a jin 'yan tawayen dake zaune a wajen, na da akala da kungiyar ta Tahris al-Sham.

Sauran sassan birnin na Homs dai na a hannun gwamnatin Syria tun Disamban 2015, lokacin da 'yan-tawaye suka fice bayan da suka kulla wata yarejejeniyar dakatar da bude wuta wadda daga bisani ta gamu da cikas.

Labarai masu alaka