Jordan ta rataye mutum 10 saboda aikata ta'addanci

Ofishin jakadancin Jordan a Bagadaza a 2003 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jordan ta ce cikin wadanda aka kashe har da wadanda suka kai hari a shekarar 2003 kan ofishin jakadancin kasar a Bagadaza

Kasar Jordan ta kashe fursunoni 15, ciki har da mutum 10 da aka samu da laifin kai hare-haren ta'addanci.

Fursunonin, wadanda duka 'yan kasar ta Jordan ne an rataye su ne da sanyin safiyar ranar Asabar a Amman, babban birnin kasar.

Ragowar biyar din da ba a samu da laifin ta'addanci ba an kashe su ne saboda laifin fyade da cin zarafi.

Wannan ne kisan fursunoni mafi girma da aka yi a Jordan a cikin shekaru masu yawa.

Kasar ta dakatar da aiwatar da kisan kai na wucin-gadi tsakanin shekarun 2006 da 2014.

Masu aiko da rahotanni sun ce sauyin da aka samu na da alaka ne da yawaitar miyagun laifuka da kuma barazana daga kungiyoyin masu fafutikar jihadi irinsu IS.

Jordan na daya daga cikin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da suka ci gaba da aiwatar da hukuncin kisan kai.

Labarai masu alaka