Mexico za ta taimakawa 'yan kasar mazauna Amurka

Shugaban Mexico Enrique Pena Nieto
Bayanan hoto,

Tun bayan hawan shuga Trump mulki Amurka da Mexico ke zaman 'yar tsama saboda batun gina katanga tsakaninsu da taso keyar baki 'yan ciranin Mexico zuwa gida

Wata jami'a mafi girma a kasar Maxico ta sanar da shirin taimakawa baki 'yan cirani ma kasar da ke zaune a Amurka.

The National Autonomous University of Mexico UNAM, ta ce za ta fara bada tallafin ta hanyar bin ka'idoji a cibiyoyin ta biyar da ke Amurka, ga dubban 'yan cirani, wadanda suka shiga kasar ta barauniyar hanya tun su na kanana.

Harwayau, UNAM ta ce za ta taimakawa irin wadannan mutanen samun takardar zama 'yan kasa, da kuma ba su guraben karatu a sahen yaki da wariyar launin fata, da sanin hakkin dan adam da kuma ayyukan ci gaban al'uma.

Jami'ar ta ce za ta gudanar da wannan aikin taimako ne, tare da tallafin gidauniyar fitaccen attajirin kasar Carlos Slim.