Taliban na son jama'ar Afghanistan su dasa bishiyoyi

Wasu mayakan Taliban a lardin Herat a 2016
Bayanan hoto,

An umarci mayakan Taliban da su shuka bishiyoyi

Shugaban kungiyar mayaka ta Taliban a Afghanistan, Hibatullah Akhundzada, ya nemi 'yan kasar da su dasa bishiyoyi.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, shugaban ya yi kira ga fararen hula da kuma mayakan sa-kai na Taliban din da kowanne ya dasa bishiya akalla guda daya domin kawata duniya da kuma amfanin halittun da Allah ya yi.

Afghanistan dai na fama da matsananciyar matsalar sare bishiyu domin yin itace da azarar gini.

Ba dai kasafai 'yan kungiyar Taliban suke fitar da sanarwa ba irin wannan.

wannan sanarwa dai wadda kungiyar ta fito da ita ranar Lahadin nan ta sha banban da irin galatsi da sakonnin barazana da kungiyar ke aike wa gwamnatin kasar da dakarun tsaro na NATO masu mara wa gwamnati baya.

Ana yi wa Akhundzada, wanda ya zamo shugaban kungiyar a watan Mayun da ya gabata, kallon malamin addini fiye da kallon mayakin sa-kai.

Akhundzada ya ce "Shuka bishiya wani abu ne mai mahimmanci wajen kare muhalli da habakar tattalin arziki da kuma kawata duniya."

"Shuka bishiya da noma na da matukar amfani a nan duniya sannan kuma akwai sakayya ranar gobe kiyama." In ji Akhundzada

Bayanan hoto,

Yawancin 'yan Afghanistan na amfani da itace wajen girki

An dai fi alakanta kungiyar Taliban da noman ganye mai sanya maye da gwamnati ta haram, a inda kungiyar take karbar harajin kan noma ganyen a yankunan da take iko.

Tun 1996 kungiyar ta Taliban take iko da mafi yawancin kasar Afghanistan har zuwa lokacin da sojin hadaka da Amurka ta jagoranta suka fatattake su a 2001.

Bayanan hoto,

Shugaban Taliban, Hibatullah Akhundzada dan Kandahar ne

Hakan ne ya sanya gwamnati take ta neman 'yan kungiyar da su shiga a dama da su a gwamnati amma sun sha yin watsi da hakan.

Ana kuma tunanin kasancewar sojojin kasashen waje a kasar ne ya sanya 'yan kungiyar kara bujirewa.