An ceto Jamusawan da aka sace a Nigeria

'Yan sanda sun ce za su yi kokarin ganin an ceto mutanen lafiya lau Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan sanda sun ce za su yi kokarin ganin an ceto mutanen lafiya lau

Jami'an tsaro a Najeriya sun ceto wasu Jamusawa guda biyu, da aka yi garkuwa da su a yankin Kagarko da ke jihar Kaduna.

A ranar Laraba ne dai rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da yin garkuwa da Farfesa Peter Breunig da Johannes Buringer wadanda suka kwashe fiye da shekara goma suna nazari kan kayan tarihin al'ummar NOK da ke yankin.

Su dai mutanen biyu masu nazari ne kan tarihi na abubuwan da ke binne a karkashin kasa.

Sai dai kuma wasu jami'an gwamnati na cewa turawan sun yi kuskure wajen shiga dajin ba tare da neman tallafin jami'an tsaro ba.

Yanzu dai gwamnatin jihar Kaduna ta mika mutanen ga ofishin jakadancin kasar Jamus da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Ku saurari hirar da Usman Minjibir ya yi da Yakubu Yusuf soja, mai ba wa gwamnan jihar Kaduna shawara kan harkokin tsaro kuma shugaban rundunar Operation Yaki ta jihar.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Yadda aka ceto Jamusawan da aka yi garkuwa da su