Kuskuren da aka yi wajen karrama fim din da ya yi fice

Faye Dunaway da Warren Beatty
Bayanan hoto,

Yadda Beatty ta rasa abun da zai ce bayan da ya bude ambulan

Fim din 'Moonlight' ne ya lashe kyautar fim din da ya fi kowanne kyawun hotuna a 2017, da ake yi wa taken 'Oscar Awards', sabanin sanarwar da fitacciyar jarumar fim din nan 'yar Amurka, Faye Dunaway ta yi da farko cewa 'La La Land' ne ya ci kyautar.

Da farko dai sai da aka damka wa fardusan fim din na 'La La Land', Warren Beatty kyautar, kuma jam'ar La La Land na tsaka da yin godiya ne aka fahimci cewa an tafka kuskuren.

Kamfanin PriceWaterhouseCooper ne dai ya dauki alhakin wannan kuskure kasancewar shi ne ya yi kidayar kuri'un da aka kada wa kowane fim.

A wata sanarwa da ya fitar, kamfanin ya ce: " Muna matukar neman afuwa ga fim din Moonlight dangane da kuren da muka yi wajen kidaya."

"An ba wa mai gabatarwa takardar ambulam din da ba ita ya dace a ba ta ba kuma da muka gano dandanan muka gyara. Yanzu haka muna bincike kan yadda wannan abu ya afku sannan muna bayyana rashin jin dadinmu."

Bayanan hoto,

Yadda wasu suka ji ba dadi lokacin sanarwar

Bayanan hoto,

Yadda Beatty ta rasa abun da zai ce bayan da ya bude ambulan

Bayanan hoto,

Fardusan Moonlight, Barry Jenkins da na La La Land, Jordan Horowitz suna rungumar juna

Bayanan hoto,

Jaruman da suka samu nasarar lashe kyauta