Tsangwamar da na sha saboda ni mata-maza ne — Julius

Zanen Julius lokacin yana yaro

Asalin hoton, Open Society Foundations

An haifi Julius Kaggwa da gabban jima'i na mata da maza, al'amarin da ya sanya aka yi ta tababa cewa shi mace ne ko namiji.

Irin wadannan mutane dai na fuskantar wahalar zama a cikin al'ummar da ba ta son sauyi a kasar ta Uganda.

"An yi min lakabi da 'Julia' amma kullum ina yi wa kaina kallon namiji". In ji Julius, mai shekara 47.

Lokacin da cika shekara bakwai ne ya fara fahimtar cewa gabbansa na da banbanci da mafi yawancin yara.

Ya ce "Banbancin ba shi da yawa sai dai kuma ya janyo minb abin kunya".

Mahaifan Julius talakawa ne manoma kuma malaman addinin kirista ne.

Mahaifiyarsa ta kasance mai nuna masa kauna da ba shi kariya kamar yadda yake fadi "Iyalina sun rungume ni hannu biyu ba tare da wani sharadi ba".

'Shin haihuwar mata-maza bala'i ne?

Julius ya ce halitta irin ta mata-maza ba abu ne da za a dauka karami ba a kasar Uganda.

"Bisa al'adarmu, mata-maza wani abu ne da za a iya daukar sa a matsayin bala'i ko kuma abin kunya sannan kuma abun neman tsari."

Asalin hoton, Open Society Foundations

Bayanan hoto,

Zanen mahaifiyar Julius lokacin da wani lokaci take kebe shi daga cikin yara

Duk da yake ba a kange Julius a cikin gida ba kamar yadda ake yi wa masu irin halittarsa, amma har yanzu yana tuna yadda a lokacin ake zaunar da shi a gida domin kebewa daga mutane.

"Mafi yawancin lokuta mahaifana na hana ni yin wasu nau'in wasanni domin guje wa wulakanci da tozatawa." In ji Julius.

Ya ci gaba da cewa "Kuma saboda irin kariyar da mahaifiyata take ba ni ya sa na yi ta sauya makaranta. ba dadi domin ina jin kamar an ware ni saboda na sha wahala wajen samun abokai."

Mahaifiyar Julius tana kai shi wurin masu maganin gargajiya domin neman waraka. Sai dai kuma maganin bai ci ba.

Asalin hoton, Open Society Foundations

Bayanan hoto,

Yadda ake kai Julius wurin masu maganin gargajiya

"A lokacin da nake shekara 11, sai da dage sosai domin samun shiga makarantar mata ta kwana ta Anglican, saboda mahaifiyata tana tunanin na je tudun-mun-tsira to amma sai abun ya fi na da".

"Lokacin da muka balaga, matan suna yin abubuwa kamar kitso da batun soyayya da na jima'i da dai sauransu amma ni ba ni da sha'awar su.

" Na fara jin ina sha'awar 'yan mata, al'amarin da ya daure min kai saboda ba zan iya magana a kan hakan ba."

Mene ne mata-maza?

Mata-maza su ne wadanda ake haihuwa da gabban jima'i na maza da na mata.

Wasu alkaluman Majalisar Dinkin Duniya dai sun nuna cewa akan samu masu halittar mata-maza a cikin mutane kaso 1.7 na al'ummar duniya.

Lokacin da Julius ya cika shekara 16, ta bayyana cewa shi namiji ne. Muryarsa ta yi girma sannan gashinsa ya sauya zuwa na maza.

Julius ya ce " A wannan lokaci, na shiga tsaka mai wuya", " dole na bar makarantar 'yan matan da nake."

Asalin hoton, Open Society Foundations

Bayanan hoto,

Yadda jikin Julius ya fara sauyawa zuwa na maza a lokacin da ya balaga

Julius ya bar Uganda, a inda ya koma Kenya domin ci gaba da karatunsa. Kuma bisa shawarar likitansa, ya daina daukar kansa a matsayin jinsin mace.

" Na cire duk wani tinanin ni mace ce, a inda na amince da zama da namiji," in ji Julius.

"Ba karamin abu ba ne a harkar zamantakewar dan adam ka koma namiji daga mace."

Barazanar da Julius ya fuskanta

Bayan da Julius ya gama karatu a Kenya, ya koma Uganda a matsayin namiji ba mace ba kamar yadda aka san shi wato Julia.

Da farko, Julius ya yi sojan gona a matsayin dan uwansa amma daga baya sai mutane suka gano cewa a Julia ce.

Asalin hoton, Open Society Foundations

Bayanan hoto,

Lokacin da labarin Julius ya bayyana a jarida

Daga nan ne kuma sai ya fara fuskantar barazana.

wasu mutane sun labarta wa wani gidan jarida a kan Julius kuma kafin ka ce kwabo labarinsa ya baza duniya.

"Na samu barazana mai yawa daga labarai."

"Abion da wasu ke fadin ma shi ne wai na sauya jinsina na mace zuwa namiji a saboda haka ya kamata a kone ni."

Asalin hoton, Open Society Foundations

Bayanan hoto,

Julius ya samu aiki a Afirka ta kudu

irin wannan barazana ce ta sanya Julius barin kasar tasa a karo na biyu, a inda ya koma kasar Afirka ta Kudu.

Wani abokinsa ya taimaka masa wajen samun aiki a kamfanin yin manhajojin komfuta wanda yake biyan ma'aikatansa kudi masu yawa.

"Wannan ne ya ba ni damar zama a can har zuwa wasu 'yan shekaru," in ji shi.

Batun mata-maza a talbijin

Katsam wata rana ina jujjuya tashoshin talbijin sai na ga wata tashar Uganda na tattaunawa kan wani yaro mata-maza.

"Wannan ne ya sa na damu har na yanke shawarar komawa gida domin na taimake shi."

Asalin hoton, Open Society Foundations

Bayanan hoto,

Julius ya yi kare hakkin mata-maza a gidan talbijin

Ina Julius?

Yanzu haka dai Julius, wanda ya riga ya yi aure kuma yana da 'ya'ya guda hudu, na aiki ne a matsayin shugaban kungiyar kare hakkin mata-maza a Uganda.

Ya kasance mai fafitikar fadakarwa kan mata-maza, a inda yake aiki tare da ungozomomi kan kawo karshen kin jinin mata-maza.

Julius yana kuma son a fito da dokokin da za su haramta wulakanta sannan su kyautata rayuwar mata-maza.

Asalin hoton, Open Society Foundations

Bayanan hoto,

Julius yana fadakarwa kan illar kin jinin mata-maza

Asalin hoton, Open Society Foundations

Bayanan hoto,

Zanen Julius da matarsa da 'ya'yansa hudu