Yadda 'yan mata ke zabar mijin aure a Chadi

Yadda samari 'yan kabilar wodaabe ke caba ado tare da kure-adaka domin burge 'yan mata a bikin rawar Gerewol

Samarin wodaabe na rawar al'alda

Asalin hoton, Tariq Zaidi

Bayanan hoto,

Samarin Wodaabe suna rawar "Yaake" wata rawar al'ada a yayin taron al'ada inda suke caba ado don 'yan mata su zabi wanda ya fi birge su don ya zama mijin aurensu. Wannan ce kadai al'adar da ke bai wa 'yan mata damar zaben miji a Afirka, kazalika al'adar ta bai wa matan aure ma damar zabar wanda suka ga ya musu don ya dinga debe musu kewa, wato kwarto.

Asalin hoton, Tariq Zaidi

Bayanan hoto,

Wodaabe na nufin “al'umma masu camfi” - wadansu rukuni ne na kabilar Fulanin Bararo, wadanda suka warwatsu a kasashen Afirka shekaru aru-aru. A nan wani mutum ne dan kabilar ta Wodaabe ya tashi da asuba a cikin daji, a dan karamin muhallinsa ga kuma jakunansa a kusa da shi.

Asalin hoton, Tariq Zaidi

Bayanan hoto,

'Yan kabilar Wodaabe yawanci sun dogara ne da fura da nonon da suke tasa daga dabbobinsu sannan kuma da naman tumaki da awaki a wasu lokuta na musamman. A nan wasu yara ne ke kada kindirmo a cikin gora domin mayar da shi nono

Asalin hoton, Tariq Zaidi

Bayanan hoto,

Nan samari ne ke ta shiryawa don yin rawar Gerewol a jajiberin ranar bikin. Rana ce da ake matukar jiranta da dokin zuwanta, kamar yadda a wasu shekaru ake ganin akalla mutum 1000 sun halarci bukukuwan. Samarin su kan caba ado ne a fuskokinsu da kayan ado kamar su hoda fankeke, da sauran kayan ado irin na al'ada. Wasu samarin kuma kan shafe labbansu da bakin fenti domin fito da fararen hakoransu.

Asalin hoton, Tariq Zaidi

Bayanan hoto,

Wannan wani saurayi ne ke taka rawar gerewol inda yayi gyaran fuska domin fito da goshinsa, kuma yana jujjuya idanunsa tare da yashe hakora a wani bangare na rawar, wadda ke daukar hankalin matan al'ummar.

Asalin hoton, Tariq Zaidi

Bayanan hoto,

Mutanen Wodaabe na shan hantsi a gidajensu kan gadajensu na kara. Haka kuma suna kwana ne tare da iyalansu baki daya.

Asalin hoton, Tariq Zaidi

Bayanan hoto,

Dan kabilar Wodaabe na zuba shayinsa da safe. Shan shayin dai na da matukar muhimmanci a al'adar tasu. Haka ma a lokacin rawar gerewol samarin kan sha shayin wanda aka yi shi da wasu abubuwan kara kuzari wanda kuma ke taimaka musu a lokacin rawar tasu

Asalin hoton, Tariq Zaidi

Bayanan hoto,

Shiryawa bukukuwan Gerewol abu ne na hadin kai sannan kuma mutane kan taimakawa 'yan uwansu domin kwalliyar tasu ta fito fili sosai. Lokutan da samarin ke dauka don yin adon nasu da tufafin nasu ne ya sa ake kiransu da Wodaabe, wato kwakkyawar kabila.

a

Asalin hoton, Tariq Zaidi

Bayanan hoto,

An tabbatar da cewa wadansu kayan kwalliyar suna da matukar wahalar samu don haka ana tafiya mai nisan zango domin samo su. Misali wata hodar fuska ana samunta ne kawai a wasu duwatsu da ke yankin tsakiyar kasar Nijar. Haka kuma wasu kabilun kan dauki akalla tafiyar nisan kilo mita 1,400 a kafa domin samo wasu kayan adon.

Asalin hoton, Tariq Zaidi

Bayanan hoto,

Bikin rawar ta Gerewol dai wanda sau daya ake yi a shekara, ya sa haka ana da matukar dokin zagayowarta domin samun matar aure na da matukar muhimmanci.

Asalin hoton, Tariq Zaidi

Bayanan hoto,

A daren jajubirin bikin, samarin Wodaabe kan ware wasu 'yan mintuna domin duba irin kwalliyar tasu a madubi,domin ganin dacewarsu. Suna kallon madubin akai-akai.

Asalin hoton, Tariq Zaidi

Bayanan hoto,

Duk da cewa mata basa yin kwalliya kamar maza, to amma zuwan nasu na kara wa wajen armashi. Su kan yi kitso tare da yi wa gashinsu kwalliya. Tsagar da ke fuskar wannan yarinya an yi mata ne tun tana karama kuma yana nuni ne da kabilar da ta fito.

Asalin hoton, Tariq Zaidi

Bayanan hoto,

Samarin Wodaabe ke nuni da fararen hakoransu lokacin da suke rawa. Gashin jiminar da ke hularsu na dada fito da tsawonsu

Asalin hoton, Tariq Zaidi

Bayanan hoto,

Samari da yaran Wodaabe a kan dogon layi sanye da fatar jauhari da huluna masu dauke da gashin tsuntsu masulauni daban-daban gaba da baya.

Asalin hoton, Tariq Zaidi

Bayanan hoto,

Wasu samari biyu kenan ke hutawa bayan sun tiki rawa. Bikin Gerewol biki ne da ake gwada karfin halin maza, wanda za su yi rawa har na tsawon sa'o'i ba tare da sun nuna gazawa ba, da zummar burge mata.

Asalin hoton, Tariq Zaidi

Bayanan hoto,

Wannan wani lokaci ne a karshen bikin, nda a gefen hannu mace ta zabi saurayinta yayin rawar. Hakan na faruwa ne cikin wayo da kuma sauri, ba za ma ta iya kallonsa da idanunta ba. Bikin lamari ne da ya shafi kabilu da dama inda mataye ke zabar samari daga kabilu daban-daban.

Asalin hoton, Tariq Zaidi

Bayanan hoto,

A lokacin da rana ta kusa faduwa gashin jiminar da samarin kan sanya a hulunansu kan zama kamar bishiyar dabino, wanda ke sanya samarin su zama gajeru da dogayen mutane. Idan bikin ya kare Wodaabe kan koma ne ayyukansu na yau-da-kullum na kiwon shanu.

Pictures and words by Tariq Zaidi.