Mosul: Yadda aka yi ruwan bama-bamai a fagen daga

An Iraqi man and woman, who look to be struggling, walk amid dust and sand as they flee their homes in west Mosul. Dozens of people, including children are seen behind them.
Bayanan hoto,

Fararen hula na tserewa daga yammacin Mosul yayain da ake kazamin fada tsakanin dakarun Iraki da masu ikirarin kafa daular Muslunci

A karshen makon da ya gabata ne kimanin mazauna birnin Mosul 2,500 suka tsere daga Yammacin birnin, wanda ke karkashin ikon kungiyar da ke ikirarin kafa daular Musulunci IS, na tsawon shekara uku.

Kungiyoiyin bayar da agaji sun yi kiyasin cewar kimanin mutum 750,000 aka yi wa kawanya a Yammacin Mosul, wadanda suka kasa tserewa daga birnin, duk da cewa akwai yiwuwar nan gaba a yi ba-ta-kashi mai tsawo na neman iko da birnin tsakanin dakarun gwamnatin Iraki da mayakan IS.

Zuwa yanzu hare-haren da ake kai wa a Yammacin Mosul sun yi tsanani kamar yadda aka zata -- sojojin Iraki wadanda suka samu isasshen horo da kuma wadatattun kayan yaki suna dannawa cikin birnin, domin karfinsu da kuma hare-hare sama na dakarun kawance da ke taimaka musu.

Duk da musgunawa mutane da mayakan IS ke yi da rashin hakurinsu, suna nuna tsagoran basira a yakin, ta inda a baya-bayan nan suke kaddamar da dabarun yakin da kusan ba a taba amfani da su ba a duk wani yaki da aka taba yi na cikin gari a zamanin nan. Suna amfani da jirage marasa matuka inda suke jeho bama-bamai da gurneti kan fararen hula da sojoji.

Hakika rundunonin soji a gabas ta tsakiya sun yi amfani da manyan jirage marasa matuka wanda galibinsu ke haddasa asarar rayuka.

Amma yawan hare-hare da kuma yadda mayakan IS ke sarrafa kananan jirage marasa matukan wajen kai hare-hare bam a Mosul, yasa dakarun gwamnati sun jinkirta dananwar da suke yi cikin birnin.

Bayanan bidiyo,

The Islamist group say this shows their drone attack on Mosul

Jirage marasa matukan kuma sun sa fararen hula, ciki har da mazauna gabashin Mosul, gigicewa. An kwato wannan bangaren birnin daga mayakan IS a watan jiya a matakin farko na yakin korar masu kaifin kishin Islaman daga sansaninsu na karshe a Iraki.

A wani asibiti a brinin Irbil da ke arewacin Iraki, wakilin BBC ya hadu da Umm Mohammed mai shekara 55, tana kuma da 'ya'ya bakwai, wadda 'yar asalin gabshin Mosul ce, tana zaune ne kan gadon asibiti inda ake sa mata ruwa. Ba ta iya kwanciya saboda tsananin ciwon da kafarta ta dama ke yi.

Ta ji rauni ne a kafarta sakamakon fadowar bam daga jirgi marasa matuki.

Bayanan hoto,

Umm Mohammed tana samun sauki a Irbil bayan ta ji ciwo a wani harin jirgi mara matuki wanda IS ta kai

Ta bayyana wa wakilin BBC cewar: "Na je kasuwa ne kawai in yi wata sayayya... Kawai sai na ji ina kwance a kasa ina kallon sama. Mutane suna ishara da zuwa sama inda bam din ya fado. Ina jami'an tsaro lokacin da wadannan jiragen ke shawagi a sama suna kashe mu?"

Tasirin hare-haren a halayyar mutane

Amfani da jirage marasa matuka da kuma araharsu ba za su sauya yadda rikicin nan ke tafiya ba.

Akwai dubban makamai wadanda suka fi tsada da hatsari wadanda ake kaddamarwa kullum a wannan rikicin.

Duk da haka ba za a iya kore tasirin amfani da jirage marasa matuka da ake amfani da su a rikicin ba, inji Emanuele Nannini daga hukumar bayar da agajin gaggawar Italiya, wadda ke kula da asibitin da Umm Mohammed da kuma sauran wadanda hare-haren bam din jirage marasa matuka suka shafa ke samun kulawa.

"A zahiri, daya suke da harin roka, amman sun fi samun inda aka harba su," inji Mista Nannini, wanda ya fadi haka a lokacin da yake sa ido a shirin gaggawa na fadada gadaje da kuma dakunan asibitin domin yakin da ake yi a yammacin Mosul.

"Saboda haka ko wanne daga cikin jirage marasa matukan nan na samun inda aka yi hako. Ta fannin halayya abu ne mai wuya ga mutane saboda za su iya kai hari a ko wani lokaci da kuma ko wani wuri," inji shi.

Mazauna gabashin Mosul suna samun hutun kankanin lokaci daga hare-haren jirage marasa matukan saboda mayakan IS sun mayar da hankalinsu kan sabbin fagen yaki a kudanci da yammacin birnin.

Bayanan hoto,

IS ta karbi iko da birnin Mosul a watan Yunin shekarar 2014 kuma yanzu shi ne sansaninta na karshe a Iraki

Wani abokin aikin wakilin BBC da ya dawo daga ziyarar aiki a fagen dagar a karshen mako, ya siffanta masa yawan hare-hare bama-baman jirage marasa matuka da ruwan bama-bamai kan dakarun da ke son shiga birnin.

Bayanan hoto,

Wasu sojojin Amurka na cikin masu gwabza fada a yakin neman iko da yammacin Mosul

Kwamandan runduna ta daya ta sojin dawakin Amurka Laftanar Kanar John Hawbaker, "Yakin Mosul zai kasance babban kalubale ga ko wacce rundunar soji, amman wannan yakin zai kare ne kawai da sakamako daya."

Suna kuma samun taimako da shawarwari daga dakarun kawance na wasu kasashen.

A sansanin da wakilin BBC ya ziyarta kilomita kadan daga yammacin Mosul, manyan tankokin Amurka masu sulke sun harbi mayakan IS a ciki da kusa da birnin da aka yi wa kawanya.

Karfin Iko: daga 24 ga watan Fabrairun shekarar 2016

Sojojin sun shaida wa wakilin BBC cewar rannan ne ranar da suka fi aiki tun farkon fara fadan, inda suka yi ta wurga daruruwan bama-bamai ga wasu wurare.

Manyan makaman Amurka ba za su yi amfani sosai ba a lokacin da yakin ya koma tsukakkun layukan birnin Mosul masu kwane-kwane.

A ranar farko na yakin a bangare yamma, dakarun gwamnati sun ba da sanarwar cewar sun samu gomman tarkon bama-bamai. An kwance wasunsu amma wasu sun tashi inda suka kashe da kuma jikkata wasu sojojin Iraki.

Bayanan hoto,

Mutuwar soji da fararen hula na Iraki na karuwa a lokacin da dakaru ke dannawa cikin yammacin Mosul

A cikin hargitsin ne fararen hula a birnin Mosul din ke ganin abubuwan tsoron da mutum ba zai iya tunani ba a ko wacce rana.

Hafsoshin sojin Amurka da na Iraki sun ce yakin zai kasance na gida-gida a gine-ginen da mayakan IS suka sanya kawunansu cikin farare hula inda suka gina ramukan tafiyarsu da kuma safarar makamai.

A wajen garin, masu aikin jin kai sun jira cikin fargaba. Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tana gina sabbin sansanonin a kudancin inda ta ke shirin karbar kimanin mutane 250, 000 da aka raba da muhallansu.

Amma asalin abin fargaba, yadda wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya shaida wa wakilin BBC, shi ne yawancin mutane ba za su iya tsira ba.

Za su kasance cikin birnin Mosul ne har sai fadan ya kare a lokacin da aka daina jin harcin bindiga kuma aka ci kungiyar IS a yaki.