Ana karancin ruwan nono a tsibirin Ireland

Ireland

Asalin hoton, Thinkstock

Bayanan hoto,

Cibiyar tara ruwan nono ta ce mata masu shayarwa na bayar da gudunmuwar ruwan nononsu

Wata cibiyar tara ruwan nono a tsibirin Ireland ta yi gargadin cewa ana karancin ruwan nono a kasar.

Cibiyar tara ruwar nono ta Fermanagh a Irvinestown na samarwa dubban jarirai gudunmawar ruwan nono.

Manajar cibiyar, Ann McCrea, ta ce suna da ruwan nono na sati biyu don haka suna kira ga mata masu shayarwa su bayar da gudunmawar ruwan nononsu.

Ann McCrea ta ce cibiyar na daya daga cikin dalilian da wasu jarirai suka rayu.

Ta kara da cewa a wasu lokuta, gudunmawar ruwan nono ne ke "bambanta tsakanin rayuwa da mutuwar jariran."

Shekara 17 da ta wuce ne gidauniyar Western Health and Social Care Trust ta bude cibiyar tara nono ta Fermanagh domin samar da nono ga sashin kula da jarirai sababbin haihuwa a tsibirin Ireland.

A bara, ta bai wa jarirai fiye da 900 ruwan nono, da kuma jarirai 50 a bariya.

Manajar ta ce tana ganin cewa karuwar jariran dake bukatar ruwan nono ya danganta da fahimtar amfanin sa.

Ann McCrea ta ce bangaren kula da jarirai sababbin haihuwa na bukatar taimakon ruwan nono saboda yana kunshe da kuzari da kuma wasu sinadaran da jariran ke bukata domin su girma cikin koshin lafiya.