Takacin da matan 'yan ci rani ke sha a Indiya

Chandigarh
Bayanan hoto,

Yawancin matan da suka taru a nan an ci zarafin su ko kuwa mazansu sun yi watsi da su

A wani boyayyen waje a garin Chandigarh, ana gudanar da wani taro na musamman cikin sirri.

Mata da dama daga yankin Punjab na tafiya zuwa babban birnin kasar domin neman taimako a wurin Amanjot Kaur Ramoowalia - shugabar kungiyar da ke bayar da taimako ga matan da mazajensu suka gudu suka bar su cikin mawuyacin hali.

Ms Ramoowalia ta ce akwai mata fiye da 15,000 a jihar da suka tsinci kansu a cikin wannan yanayi.

Ta kara da cewa, "Ina kula da kusan mata 15 a duk wata, wadanda mazansu suka bar su cikin halin ka-ka-ni-ka-yi, a kullum kuma alkaluman na karuwa."

Ms Ramoowalia ta shaidawa BBC cewa, ta sha ganin mata kyawawa, masu kaifin basira cikin mummunan hali na kunci.

"Suna kunyar zama a cikin al'umma a matsayin su na matan da mazansu suka yi watsi da su, wanda hakan tamkar an take masu hakkokinsu ne." In ji Ms Ramoowalia.

Bayanan hoto,

Ms Ramoowalia ta shafe shekara goma tana aikin kula da wadannan mata da mazan su suka yi watsi da su

'Kudi ya fi soyayya'

Mazajen dai 'yan kassshe daban-daban ne daga ko ina a fadin duniya, amma yawancin su 'yan Kudancin Asiya ne, mazauna kasashen Birtaniya da Amurka da Canada.

Matan na yarda da auren ne, da tsammanin inganta rayuwarsu a kasashen waje.

Amma su kuwa mazan babban burinsu su samu kudi ne ba wai soyayya suka sa a gaba ba.

Ana zaton kashi daya daga cikin uku sun fito ne daga Birtaniya.

Ms Ramoowalia ta ce: ''Angon yana zuwa ne, ya karbi sadaki mai dumbin yawa.

"Sai an daura auren, ya karbi kudin ya mori amarci, idan ya koma kasarsa ba a sake ganinsa"

Bayanan hoto,

Taro da aka gudanar a Chandigarh

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

''Ina da juna biyu lokacin da mijina ya watsar da ni''

A kasar Indiya, al'ada ce iyayen amarya su bai wa ango kudi ko wata kyauta, duk da cewa an haramta wannan al'ada tun 1961.

Ana biyan sadakin dubban fam-famai.

Daya daga cikin matan da suka halarci taron, ta zo ne daga wani kauye da ke wajen garin Punjab.

Kamaljit Kaur ta auri wani mutum dan kasar Italiya shekara uku da suka gabata. Amma bayan wasu watanni sai ya gudu ya bar ta.

A lokacin tana dauke da cikin dansa.

"Jim kadan bayan auren sai ya fara gunagunin karancin sadakina, har da cewa wai iyayena ba sa farin ciki da ni."

A karshe dai, mijin Kamaljit ya bar kasar ya koma Italiya. Bata sake ganin sa ba.

Ta haifi 'yarta da rashin lafiya, amma sai 'yan uwan mijin suka ki taimakon ta.

"Suka ce tun da yarinyar naƙasasshiya ce to su ba sa bukatar ta, don 'ya'yan da suke da su a zuri'arsu sun isa haka.

Abin bakin cikin shi ne, 'yar Kamaljit ta mutu bayan wasu watanni, amma duk da haka mijinta bai tuntube ta ba.

Bayanan hoto,

Kamaljit Kaur ta ce mijinta ya yi watsi da ita da 'yarta mara lafiya

''Nawa mijin ya yi watsi da ni tsawon shekara 16''

Hanyar da ake bi wajen sakin mijin da ba dan kasar Indiya ba na da ahala da kuma tsada.

Sau da yawa 'yan uwan matar hakan ke yi wa matukar illa.

'Yar wani mutum mai suna Darshan ta yi aure tun shekarar 1997, amma har yanzu ba a kashe auren ba.

"Mijin bai ce komai ba sai da ya zo tafiya. Ya ce, yana da mata a wata kasar. Yana da 'ya da kuma dansa, don haka ba zai iya tafiya da 'yarmu ba. Ku yi duk abin da ku ka ga za ku iya.

Mun dau matakin zuwa kotu amma har yanzu ina cikin wannan matsala shekara 16 ke nan"

Daljit Kaur lauya ce ta kwamitin da ke kare hakkokin 'yan kasar waje a jihar Punjab, wadda ke kula da shari'ar 'yar kasashen ketare.

Ta bayyana cewa "Ana jikiri wurin shari'a, don haka za a iya daukar shekaru da dama ba a yanke shawara ba.

"Akwai matsaloli da dama kuma wadannan 'yan mata ba su da kudin da zasu iya biya na shari'ar."

Bayanan hoto,

Ms Ramoowalia ta ce mata da aka yi watsi da su na rayuwa cikin kaskanci

Rayuwa Cikin Kaskanci

A garin Chandigarh, Amonjot Kaur Ramoowalia na bai wa mata da dama da suka shinci kansu cikin wannan hali shawarwari.

Amma taimakon da zata iya ba su ragagge ne.

Duk da cewa laifi ne a Indiya mutum ya gudu ya bar matarsa, yana da matukar wahala a gurfanar da mutum gaban shari'a in dai har ya sa kafa ya bar kasar.

Ta ce wasu daga cikin labarun ba su da dadin ji.

"Wata yarinya ta taba yin aure, mijin ya dinga takura mata wajen saduwa da ita ba ta dadin rai ba, kuma ya gudu ya bar ta da yaro. Babu wata doka mai karfi da ake bi.

"Za ta ci gaba da yin rayuwa cikin kaskanci kasancewar mijinta ya yi watsi da ita."

Ms Ramoowalia ta yi kira ga sauran kasashen waje, su san irin ayyukan da 'yan ƙasarsu ke aikatawa kuma su taimakawa gwamnatin Indiya wajen hukunta su.

A halin da ake ciki, mata da aka yi watsi da su a Indiya na rayuwa a cikin hali na rashin tabbas.