Gobara a kasuwar Mogadishu ta haddasa dimbin asara

Wani dan kasuwa dake magana da mazauna kusa da wurin da gobara ta barke

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Makwabtan kasuwar sun taimaka wajen kashe gobarar

'Yan kasuwa a Mogadishu, babban birnin Somaliya, na kirga dimbin asarar da suka tafka bayan da gobara ta lalata babbar kasuwar garin da safiyar ranar Litinin.

Gobarar, wacce ta fara daga kasuwar Bakara, ta yi ta ruruwa har tsawon da sa'oi fiye biyar kafin a kashe ta.

Gobarar ta fara ne da misalin karfe hudu na asuba kuma tun kafin wayewar gari hukumomi da mazauna yankin da ma wasu kamfanoni masu zaman kansu suka yi ta kokarin kashe wutar.

A cewar mazauna yankin, gobarar ta fara ne a wani bangare da ya yi fice wajen sayar da kayan gida sannan daga bisani ta bazu zuwa wasu sassan babbar budaddiyar kasuwar.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wasu 'yan kasuwar na kokarin kwashe wasu daga cikin kayansu

Duk da cewa ba a fitar da alkuluma a hukumance ba, ana zaton an yi asarar miliyoyin daloli saboda gobarar ta kona akasarin kasuwar.

BBC ta yi magana da daya daga cikin 'yan kasuwar da gobarar ta shafa.

"Mun yi asarar kasuwancinmu da dukiyoyinmu a nan. Kuma gobarar ta zo a lokacin da kasar ke kokarin shawo kan matsanancin fari da take fuskanta. Na rasa shagona. Na tsira da kaya kadan kuma ba ni kadai lamarin ya shafa ba" wannan asarar ta shafa ba.''

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Babu isassun na'urorin kashe wuta a birnin shi ya sa wutar ta bazu

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Gobarar ta yi ta ci har tsawon sa'o'i biyar

Babu isassun na'urorin kashe wuta a birnin kasancewar an yi shekara da shekaru ana yaki a kasar.

Shugaban kungiyar 'yan kasuwa da masu masan'antu ta Mogadishu, Ali Hussein Ibrahim, ya shaida wa BBC cewa a yanzu yana da matukar wuya a gano abin da ya haddasa gobarar.

''Muna fuskantar kalubale da dama a kasuwar. Misali, a wasu lokutan, mutane kan bar risho a kunne, a wasu lokutan kuma zai iya kasancewa matsala ce daga wutar lantarki wanda ba kasafai ake kula da shi ba, saboda haka, a yanzu zai yi wuya a gano musabbabin gobarar amma dai muna yin bincike.''

Ba wannan ne karo na farko da aka yi gobara a kasuwar ba, kuma masu sa ido kan al'amuran yau da kullum sun ce akwai yiwuwar a sake samun gobabrar nan gaba duba da irin rashin tsarin kasuwar da kuma rashin shirya wa aukuwar irin hakan daga bangaren gwamnati.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

'Yan sandan Somaliya ka kokarin hana mazauna yankin shiga wurin gobarar