Nigeria za ta fafata da Senegal da Burkina Faso a London

'Yan wasan Najeriya suna murnar nasarar kan Algeria

Asalin hoton, PIUS UTOMI EKPEI

Bayanan hoto,

'Yan wasan Najeriya suna murnar nasarar kan Algeria

Kungiyar wasa ta Super Eagles ta Najeriya za ta taka leda da Senegal da Burkina Faso, a wasannin sada zumunta, a watan Maris a birnin London.

'Yan wasan na Super Eagles za su kara da na Teranga Lions na Senegal a ranar 23 ga Maris sannan kuma kwana hudu bayan nan su kara da Stallions na kasar Senegal.

Wasannin dai na zuwa ne kafin wasan da Najeriyar za ta fafata da Afirka ta Kudu, a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin zakarun Afirka ta 2019, a watan Mayu.

Najeriya dai ta yi nasarar sau takwas a wasanninta da ta taka da Senegal sannan kuma sun yi canjaras a wasanni biyar, a inda kuma Senegal ta yi nasara a kanta a wasanni uku.

Sai dai kuma Najeriyar ba ta taba rashin nasara ba a kan Burkina Faso a wasanninsu da suka yi 13

Najeriya dai wadda ta dauki kofin gasar zakarun na Afirka har karo uku, ba ta samu cancantar shiga gasar ba a gasar guda da suka gabata.