Leicester ta lallasa Liverpool da ci 3-1

Jamie Vardy a lokacin da ake buga wasan
Image caption Ko a wasannin da suka gabata Jamie Vardy ya ciwa kungiyar sa kwallaye

Leicester City ta yi tsallan badake ta fito daga rukunin masu faduwa daga gasar Premier bayan da a gidanta ta doke Liverpool da ci 3-1.

Wasan wanda shi ne na farko da ta yi bayan korar kocinta Claudio Ranieri, shi ne karon farko da ta yi nasara gasar ta Premier a wannan shekara ta 2017, kuma ya sa yanzu tana ta 15 a tebur da maki 24 a wasa 26.

Ita kuwa Liverpool tana matsayi na biyar da maki 49.

Vardy shi ya ci kwallayan na Leicester City guda biyu a mintuna na 28 da na 60, a yayin da Drinkwater ya ci tashi kwallon a minti na 39.

Daga bangaren Liverpool kuma, Coutinho ne ya yi nasar saka kwallon a minti na 68.

Rishin nasarar da Liverpool ya sa ba zata kasancewa ta 3 ba,bayan kuma ta sha kashi a wasa 5 da ta buga a baya a cikin wannan gasar.

Labarai masu alaka