Obama ne ya janyo aka yi zanga-zanga a Amurka — Trump

Zababben Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ya yi amannar cewa Barack Obama ne ya kitsa zanga-zangar da aka yi ta nuna kin jinin 'yan majalisar jam'iyyar Republican, sannan kuma shi ne sanadin fitar bayanan sirri na tsaron kasar.

Mista Trump ya fada wa gidan talbijin na Fox News cewa: "Ina tunanin shugaba Obama ne ya kitsa komai saboda magoya bayansa ne suke da hannun a al'amarin."

Ya kuma kara da cewa: "Ina kuma tunanin siyasa ce ta sanya su yin hakan".

Sai dai kuma Mista Trump bai bayar da wasu hujjoji ba da ke nuna tabbacin zargin nasa.

Kawo yanzu dai tsohon shugaban Amurkar, Barrack Obama bai ce uffan ba dangane da zargin.

Kimanin makwanni biyu ne dai al'ummar wasu yankunan Amurkar suka yi wa wasu 'yan majalisar dokokin kasar na jam'iyya mai mulki zanga-zanga, yayin gana wa da su a zauruka daban-daban.