Tattalin arzikin Nigeria ya yi kasa

Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tattalin arzikin Najeriya ya ja baya

Wasu sabbin alkaluma da aka fitar sun nuna cewa tattalin arzikin Najeriya ya yi kasa da kashi 1.5 cikin dari a shekarar 2016, a yayin da kasar ke ci gaba da fama da koma baya a tattalin arziki irin wanda ba a taba gani ba.

A shekarar 2016, kasar da ta fi kowacce a girman tattalin arziki a Afirka ta shiga koma baya a karo na farko tun shekara 25 da ta gabata, sanadiyar faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya.

A wani rahoto da hukumar tattara alkaluma ta kasar ta yi, ta ce wannan koma baya da aka samu ya nuna matsalar da Najeriya ta shiga a bara, wanda ya hada da koma baya wajen kasuwanci, da matsalolin rashin wutar lantarki da faduwar darajar naira.

Masu suka dai sun ce sabbin tsare-tsaren da gwamnatin ke fitowa da su ne suka kara ta'azzara lamarin.

'Sharhi'

Wani masanin tattalin arziki kuma malami a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Muttaka Usman, ya shaida wa BBC cewa, rahoton yana nuna cewa tattalin arzikin Najeriya maimakon ya kara karsashi da ci gaba, ya rage karsashi da kuma ci gaban da ake neman a samu.

"To amma wannan ba abin mamaki bane. Saboda wannan maganar karayar tattalin arzikin Najeriya ta fara ne tun shekarar 2015, lokacin ne dukkan muhimman ayyukan da suke taimakawa ana ganin cewa tattalin arziki ya ci gaba suka fara ja baya, kamar harkar noma da harkar masana'antu da harkar ma'adinai da harkar man fetur," inji Malam Muttaka.

Ya kara da cewa, "Dukkan wadannan abubuwan suna ja baya ne in ban da harkar noma wadda ta dan karu. Wannan dai ala kulli hali na nuna cewa tattalin arzikin ba a yi masa turba wadda ita ce za ta kai mutane su gamsu ba."

Malam Muttaka yana ganin ya kamata a yi bita kan matakan da gwamnatin Najeriyar ta ke dauka domin fitar da kasar daga matsin tattalin arzikin da take ciki.

Ya kara da cewa, "Mafita ita ce farkon fari wannan tattalin arzikin na Najeriya ne. Saboda haka sai a zauna da 'yan Najeriya hazikai wadanda suka san tattalin arziki a yi tsare-tsaren da za su ciyar da kasar gaba, ba wai a kawo wasu ba daga uwa duniya wadanda ma basu san halin da tattalin arzikin ke ciki ba."

Tun a farko-farkon shekarar 2016 ne dai tattalin arzikin Najeriya ya fara fusknatar durkushewa, inda hakan ya jefa 'yan kasar cikin mawuyacin hali.

Labarai masu alaka