Babu wanda ya lashe kyautar Mo Ibrahim ta shugabanci nagari

Mo Ibrahim Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mo Ibrahim na son karfafawa shugabannin Afirka su mika mulki cikin lumana

Babu wani tsohon shugaban Afirka da ya lashe kyautar Mo Ibrahim ta dala miliyan biyar a bana - karo na shida cikin shekara 10 da ba a bayar da kyautar ba.

Ana bayar da kyautar ne ga shugaban Afirka da aka zabe, ya yi mulki nagari, ya kawo ci gaba a kasarsa sannan ya sauka daga kan mulki cikin lumana bayan wa'adinsa ya kare.

Hamshakin dan kasuwan nan na kasar Sudan, Mo Ibrahim, shi ne ya kaddamar da wannan tsari domin karfafawa shugabannin Afirka mika mulki cikin lumana.

Mo Ibrahim ya ce,''kamar yadda na sha fada a kowace shekara, da gangan aka tsaurara ka'idojin samun wannan kyautar. Muna yabawa rawar da wasu shugabannin Afirka suka taka wurin inganta lamura a kasarsu.

Amma manufar kyautar ita ce fitowa fili da kuma yabawa shugabannin da suka taka rawa da bakasafai a kan taka irin ta ba.''

Wadanda aka auna cancantarsu domin samun wannan kyauta su ne shugabannin da suka bar mulki daga shekarar 2014-2016.

A wannan lokaci, tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sauka daga ragamar mulki a watan Mayun 2015 bayan da sha kayi a zabe.

Shugaban Tanzania Jakaya Kikwete ya mika mulki a watan Nuwambar 2015 bayan shekara takwas yana mulki, sai kuma shugaban Malawi, Joyce Banda da ta sauka daga ragamar mulki a watan Maris din 2014 bayan da ta sha kaye.

Shekara biyu ke nan tun da aka ba da kyautar zuwa ga:

  • Shugaban Namibia Hifikepunye Pohamba a shekara ta 2014
  • Shugaban Cape Verde Pedro Pires a shekara ta 2011
  • Shugaban Botswana Festus Mogae a shekara ta 2008
  • Shugaban Mozambique Joaquim Chissano a shekara ta 2007

Shugaban Afirka ta Kudu, Nelson Mandela, shi ne ya fara lashe kyautar a shekara ta 2007.

Kyautar ta dala miliyan biyar an karkasata zuwa shekara 10 da kuma karin dala 200,000 duk shekara har tsawon rayuwarsu.

Labarai masu alaka