Za a kayyade sadakin rukunan mata a Nijar

Matan Nijar

Asalin hoton, Getty Images

Al'ummar garin Farey da ke yankin Dosso a jamhuriyyar Nijar suna gudanar da wata muhawara don yin nazari da kuma kayyade kudaden aure na rukunan mata.

Wata kungiya ce ta shirya gagarumar mahawarar, wadda ta samu halartar daukacin jama'ar garin da kewaye da suka hada da masu unguwanni da hakimai da malaman addini da mata da samari da 'yan mata.

Za a kayyade farashin ne daga na budurwa da bazawara sakin wawa da bazawara mai haihuwa daya, har ya zuwa wacce ta yi haihuwa sama da daya.

Wannan dai shi ne karo na farko da wata al'umma ta zauna ta yi nazari kan kudaden aure a Nijar.

Taron ya amince cewa sadakin budurwa sabuwa ful zai kasance jaka 325.

Bazawara sakin wawa za a biya jaka 200 cif

Bazawara mai da daya za a biya jaka 150

Sai kuma mai fiye da da daya za a biya jaka 100

Ga dai rahoton da Tchima Illa Issoufou ta aiko mana:

Bayanan sauti

Rahoto kan kayyade sadakin rukunan mata a Nijar