Ana samun karuwar 'yan gudun hijira a Tanzania

Wata 'yar gudun hijira Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsakanin 'yan gudun hijira 600 zuwa 1,000 ne ke isa Tanzania ko wacce rana

Kungiyar Likitoci ta Medecins Sans Frontieres ta bayyana cewa rikicin kiwon lafiya ka iya kunno kai a sansanin 'yan gudun hijira a Tanzania saboda karuwar 'yan gudun hijira dake isa kasar.

'Yan gudun hijira 290,000 wadanda kashi daya cikin hudu sun fito ne daga kasar Burundi, sun cunkushe a sansanoni uku na Nyarugusu da Mtendeli da kuma Nduta.

Sansanin Nduta, wanda aka kafa domin rage yawan mutane a Nyarugusu, a yammacin lardin Kigoma, na dauke da 'yan gudun hijira 117,000.

Wannan adadin mutanen sun wuce yawan mutanen da sansanin zai iya dauka.

Idan har aka cigaba da samun kwararar mutum 600 zuwa 1000 a kullum, to za a samu 'yan gudu hijira 150,000 zuwa watan Afrilu.

Kungiyar MSF wadda ke kula da lafiyar mutanen da ke sansanin ta ce an samu karuwar marasa lafiya da ke zuwa asibiti.

MSF ta kara da cewa cunkoso da rashin tsafta ya haddasa aukuwar cututtuka kamar zazzabin cizon sauro da gudawa da cututtuka da suka shafi numfashi da kuma matsalar fatar jiki.

Shugaban kungiyar David Nash ya ce akwai bukatar a samar da wani sansanin cikin gaggawa.

Labarai masu alaka