Fifa ta sake dakatar da Amos Adamu shekara 2

FIFA Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An haramtawa Amos Adamu shiga wasannin FIFA tsawon shekara uku a 2010

Hukumar kwallon kafa ta duniya, ta sake haramta wa tsohon jami'in kwamtin zartarwarta ,Amos Adamu, na Najeriya, shiga harkokin wasannin kwallon kafa tsawon shekara biyu.

Fifa ta ce "wannan hukunci zai fara ne, daga ranar 28 ga watan Fabrairu, na 2017."

Amos Adamu, wanda aka haramta wa shiga harkokin Fifa tsawon shekara uku daga watan Oktoba na 2010, an sake yi masa wanna hukunci ne, domin ya sake saba ka'idoji uku na Fifa.

An samu jami'in mai shekara 64 , da laifin karan-tsaye ga dokokin Fifa da suka haramta yin amfami da mukami don biyan wata bukata ta kashin kai.

Fifa ta ce karan keta haddin dokokin ya shafi "shirya wani taro a shekara ta 2010, yayin da yake matsayin jami'in kwamitin zartarwarta".