An hana sayar da Coca-Cola a India

WAsu masu fafutuka Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu masu fafutika a wasu sassan kasar ta Indiya sun bukaci a hana sayar da Pepsi da Koka-kola

'Yan kasuwa a garin Tamil Nadu da ke kudancin Indiya sun hana sayar da lemukan Koka-kola da Pepsi domin a rika sayen lemukan da ake hadawa a cikin gida.

A ranar Laraba ne dai aka fara daina sayar da lemukan wandanda manyan kungiyoyin 'yan kasuwan biyu suka bayar da shawarar a yi hani ga sayensu.

Kungiyoyin sun ce kamfanonin da suke samar da irin wadannan lemukan na amfani da ruwa mai yawa daga koguna.

Hakan kuma na sa manoma suna shan wahala wajen ban ruwa a gonankinsu a lokutan da ake fama da matsanancin fari.

Kungiyar yin lemuka ta Indiya, IBA, ta ce bata ji dadin matakin da aka dauka ba.

Kungiyar IBA, wadda ke wakiltar akasarin kamfanonin da ke yin lemuka na kwalaba, ta ce hanin da aka yi "ya sabawa shika-shikan cigaban tattalin arziki".

Kamfanin Koka-kola da na Pepsi da ke kasar sun samar wa iyalai 2,000 aikin yi kai tsaye a garin Tamil Nadu.

Yayin da a hannu guda kuma ya samar wa wasu iyalan 5,000 ayyuka a wasu bangarorin kamfanin.

Labarai masu alaka