An koro 'yan Nigeria 97 daga Afirka ta kudu

Wadanda aka taso kyayarsu daga Afirka ta kudu Hakkin mallakar hoto NAN
Image caption An koro da dama daga cikinsu ne saboda laifuka da suka shafi harka da miyagun kwayoyi

A daidai lokacin da ake ce-ce-kuce kan hare-haren da ake kai wa baki ciki har da 'yan Najeriya, Afirka ta Kudu ta taso keyar 'yan Najeriya 97 baisa zarginsu da aikata laifuka daba-daban.

A ranar Litinin da daddare ne mutane suka iso filin jirgin saman Murtala Muhammad da Legas.

Sun iso ne daga Johannesburg a wani jirgin sama mai dauke da lamba GBB710 wanda gwamnatin Afirka ta Kudun ta yi shatarsa.

Wani jami'i a hukumar shige da fice ta Najeriya ya shaida wa BBC cewar wadanda aka koro din sun hada da maza 95 da mata biyu.

Ya kara da cewa an taso keyar shida daga cikin mutanen ne saboda laikat aifukan shan miyagun kwayoyi, yayin da aka dawo da wasu 10 saboda wasu laifukan na daban.

An yi amannar ragowar sun aikata laifukan da suka shafi harkar shige da fice a kasar Afirka ta Kudu.

Jami'an da ke kula da harkar shige da fice a Najeriya sun dauki bayanan wadanda aka koro din, amma kawo yanzu babu cikakken bayani kan wuraren da suke.

Sai dai mai magana da yawun ma'aikatar harkokin cikin gida na Afirka ta kudun ya shiadawa BBC cewa, korar bata da alaka da rikicin kyamar baki da aka yi a wasu biranen karasar na baya bayan nan.

Ya kara da cewa an mayar da daruruwan mutane wadanda ba su da takardun zama, akasarinsu daga alummar dake kudancin wadanda aka kora sun hada da 'yan Pakistan da 'yan china da 'yan Bangladesh da 'yan Najeriya da 'yan Somaliya da dai sauransu.

Ya ce tsarin ne da dama aka saba kuma ya kan dauki tsawon kwanaki 60 zuwa 90 kafin a kammala shirye-shiryen mayar da mutane kasashensu.

Hakan na nufin mutanen da aka tasa kyayarsu a wannan makon, sun fara shirinsu tun bara don haka bashi da wata alaka da rikicin baya bayan nan.

Labarai masu alaka