Onnoghen ya zama sabon babban alkalin Najeriya

Onnoghen Hakkin mallakar hoto Channels
Image caption Onnoghen ya ce ba lallai bane kowane dan Najeriya ya ga alkali ba kafin gaskiya ta yi halinta

Majalisar dattawan Najeriya ta tabattar da nadin da aka yi wa mai shari'a Walter Onnoghen a matsayin babban alkalin kasar, bayan da ya shafe sa'a guda yana shan tambayoyi.

Mukaddashin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbanjo, shi ne ya gabatar da sunansa a cikin makwanni biyu da suka gabata.

A jawabin da ya yi bayan da aka tabbatar da nadin da aka yi masa, sabon babban alkalin Najeriyan, Onnoghen ya ce zai yi kokari domin ganin ya kara karfafa sashen shari'a a matsayin wani bangare mai cin gashin kansa.

Sanatoci sun tambaye shi yadda zai tabbatar da adalci ga talakawan Najeriya da kuma yadda zai tabbatar da yin shari'ar wadanda aka kama da laifin cin hanci ba tare da an bata lokaci ba.

Onnoghen ya yarda da batun da 'yan majalisar dattawa suka yi na cewa akwai cin hanci a bangaren shari'ar , amma ya kara da cewa zai kasance daya daga cikin matsalolin da zai magance.

" Za mu yi aiki domin tabbatar da haka kuma za mu kara karfin gwiwa wajen tabbatar da gaskiya a ayyukanmu," a cewar Onnoghen.

Sabon Babban jojin kasar, ya kuma yi magana a kan yadda zai karfafa bangaren shari'ar kasar a matsayin wani bangare na gwamnati mai zaman kansa wanda zai kasance wuri na karshe da 'yan Najeriya baki daya za su yi fatan samun adalci.

Kamar yadda ya furta, ba lallai bane sai kowane dan Najeriya ya ga Alkali ba kafin gaskiya ta yi halinta ba.

Onnoghen ya shaidawa sanatocin cewar : "Zamu karfafa 'yancin da muke da shi . Ba zan yi sake da wannan ba."