Liverpool ta shiga matsala bayan kashe dimbin kudade akan 'yan wasa

Roberto Firmino na Liverpool a wasansu da Swansea City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Roberto Firmino na Liverpool a wasansu da Swansea City

Kungiyar gasar Premier ta Liverpool ta shiga matsalar kudi duk da dimbin kudaden da ta samu wadanda ba ta taba samu ba.

Asarar da ta yi ta fam miliyan 19.8 ta kafin biyan haraji na shekarar 2015 zuwa watan Mayu na 2016, galibi ta auku ne sakamakon sayen manyan 'yan wasa da ta yi, da kuma kudin sallamar Brendan Rodgers, wanda ta kora a matsayin kocinta a watan Oktoba na 2015.

A cikin lokacin Liverpool ta sayi 'yan wasa 12, inda ta kashe fan miliyan 32 akan dan wasan gaba Christian Benteke, wanda tuni ya bar kungiyar, sanna ta kuma kashe fan miliyan 29 akan dan wasan gaba na Brazil Roberto Firmino.

Kudin da kungiyar take samu ya karu da fan miliyan uku zuwa miliyan 301, amma asarar da ta yi ta kai ta fam miliyan 20.

Bayan faduwar, kungiyar ta kuma samu ribar fan miliyan 60, wadda galibi daga cinikin sayar da Luis Suarez ne ga Barcelona akan fam miliyan 75.

Haka kuma kungiyar ta samu fam miliyan 49 daga cinikin sayar da Raheem Sterling ga Manchester City.

Kudaden da take samu daga tallace-tallace ya ragu da fan 700,000 zuwa fan miliyan 116, amma kuma kudin da take samu na shiga kallon wasanta ya karu da fan miliyan 3.4 zuwa fan miliyan 62, sakamakon rangadin wasan da kungiyar ta je Australia da Asia, kafin fara kakar wasa.

Kungiyar ta kuma samu karin kudin shiga kallon wasan nata, saboda ta samu shiga gasar cin Kofin Lig (EFL) da kofin Europa.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Liverpool ta samu karin kudi daga masu shiga kallon wasanta

Babban jami'in gudanar da kungiyar Andy Hughes, ya ce kungiyar wadda kamfanin Amurka na Fenway Sports Group, ya mallaka tun watan Oktoba na 2010, na ci gaba da samun gagarumar riba.