Ɗan wanke-wanke ya shiga sahun masu gidan abinci

Ali Sonko Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ali Sonko ya shafe tsawon shekara talatin huɗu a Denmark

Wani ɗan aikin ɗauko kwanuka ya zama ɗaya daga cikin masu mallakar wani hamshaƙin gidan abinci a duniya.

Ali Sonko mai shekara 62, a yanzu ya zama ɗaya daga cikin mutum huɗu da suka mallaki gidan abinci na Noma da ke Copenhagen, wanda sau huɗu yana samun lambar gidan abinci da ya fi kowanne a duniya.

Sonko, ɗan asalin Gambia, ya fara aiki ne tun bayan buɗe gidan abincin, kafin a bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin sabbin waɗanda suka mallake shi.

Wani jami'in gidan, Rene Redzepi ya faɗa wa taron 'yan'uwa da abokan arziƙin da suka je don taya murna cewa "Ali jini da tsoka ne na gidan abincin Noma," a cewar wata jaridar Berlingske ta ƙasar Denmark.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Tun lokacin da aka buɗe gidan abincin Noma ne, Ali yake aiki a wajen

Ya ce "Ba na jin mutane sun san darajar samun mutum kamar Ali a gidan abincin nan. Mutum ne da ke murmushi a ko yaushe, kuma a kowanne hali 'ya'yansa su 12 suke ciki"

A wani hoto na Mr Sonko da taƙwarorinsa sabbin manajojin gidan abincin, Lau Richter da James Spreadbury a shafin Instagram, Mr Redzepi ya ƙara da cewa: "Wannan somi ne kawai, a ƙudurinmu na bai wa ma'aikatanmu da dama mamaki a wannan gida da suka zaɓi su yi aiki tuƙuru."

Mr Sonko, wanda ya zauna a Denmark tsawon shekara 34, ya fara yin fice ne a 2010, lokacin da ya kasa zuwa birnin London da taƙwarorinsa don karɓar lambar gidan abinci mafi fice a duniya, saboda rashin samun takardar izinin shiga wato visa.

Labarai masu alaka