Wata mata ta mutu sakamakon ruƙiyya da wuta

Nicaragua Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mijin Vilma Trujillo ya je ɗauko gawar matarsa daga wani ɗakin ajiye gawawwaki

Wata matashiya a wani yanki na Nicaragua ta mutu mako guda bayan an ɗaure ta kuma aka yi zargin an jefa ta cikin wuta don cire mata aljannu.

Dangin matar sun faɗa wa kafar yaɗa labarai a ƙasar cewa mutum huɗu a ƙarƙashin jagorancin wani mutum da aka ce pasto ne sun far wa Vilma Trujillo.

Juan Rocha ya musanta ƙona Mrs Trujillo, a cewarsa aljanu ne suka rirriƙe ta a saman wuta sannan suka auka ta ciki.

Danginta sun ɗauko ta sa'o'i ta ji munanan raunuka sakamakon ƙonewa.

'Yan sanda sun kama Mr. Rocha da kuma wasu mutanen bisa zargin hannunsu cikin al'amarin.

Mijin matar, Reynaldo Peralta Rodriguez, ya ce an kai mai ɗakin tasa coci ne cikin makon jiya, lokacin da masu zuwa mujami'ar suka ɗauka cewa aljanu sun shige ta bisa zargin ta zari adda ta yi ƙoƙarin far wa mutane.

An jiyo shi yana cewa "abin da suka yi mana ba za mu yafe ba."

"Sun kashe matata, uwar 'ya'yana ƙanana guda biyu."

Wani mai magana da yawun hukumar kare haƙƙin Nicaragua, ya yi kira ga gwamnati ta ɗauki tsauraran matakai don taƙaita tasirin ƙungiyoyin addinai a ƙasar.

Labarai masu alaka