Jakadun kwamitin sulhu sun je nazari a kan Boko Haram

Antonio Guetteres
Image caption Sabon Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guetteres ya bukaci kasashe su tallafa wa yankunan da ke fama da barazanar yunwa a duniya

Jakadun kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya goma sha biyar na kan hanyar zuwa Afirka ta yamma don yin nazari kan ƙalubalen da ƙungiyar Boko Haram ke da shi kan harkokin tsaro.

Haka kuma, jami'an za su yi ƙoƙarin tantance matsalar ayyukan jin ƙai da Kamaru da Chadi da Nijeriya da kuma Nijar ke fama da su.

Manufar wannan ziyara ita ce ƙarfafa gwiwar shugabannin ƙasashen don su bijiro da wani bakandamen tsarin tunkarar barazanar Boko Haram a kan iyakokinsu.

A baya-bayan nan, Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana damuwa kan annobar yunwa da ta ce miliyoyin mutane na fuskanta a yankin tafkin Chadi.

Matakin zai kuma yi ƙoƙarin jawo hankalin ƙasashen duniya kan wannan rikici wanda jakadan Burtaniya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Matthew Rycroft ya ce galibi an kawar da kai.

Rahotanni sun ce ziyarar ka iya share fagen wani ƙwaƙƙwaran mataki daga kwamitin sulhu.

Dubun dubatar mutane ne rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu bayan ya yi sanadin mutuwar wasu dubbai a tsakanin ƙasashen.

Labarai masu alaka