An kebe masu zazzabin Lassa a jihar Borno

An gano kwayar cutar ta Lassa a jikin wata mata mai shekaru 32 a kauyen Zabarmari na jihar Borno Hakkin mallakar hoto PROF S.R. BELMAIN UNIVERSITY OF GREENWICH
Image caption Hukumomin lafiya a jihar Borno sun ce za su gudanar da feshin kashe beraye a yankin da aka samu bullar cutar zazzabin Lassa

Mahukunta a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya sun kebe mutane 38 sakamakon bullar cutar zazzabin Lassa a kauyen Zabarmari da ke karamar hukumar Jere.

Kwamishin lafiya na jihar Dr Haruna Mshelia, ya tabbatarwa da BBC cewa sakamakon gwajin samfurin jinin wata mata mai shekara 32 daga kauyen Zabarmari bayan ta kamu da zazzabi mai zafi a makon jiya ne , ya nuna cewa tana dauke da kwayar cutar ta Lassa.

Kwayar cutar zazzabin na Lassa na janyo zubar jini ga wanda ya kamu da ita, kuma beraye ne ke yada ta ga bil'adama ta hanyar kashi ko fitsarinsu da kan taba kwanuka ko abinci.

Dr Mshelia ya bayar da tabbacin cewa ma'aikatar lafiya ta jihar ta ankarar da masu ruwa da tsaki da suka hada da shugabannin addinai da na al'ummar yankin, a kan su wayar da kan jama'a game da muhimmancin tsaftar muhalli da ta abinci.

Ya ce ya zuwa yanzu matar ta fara samun sauki, don kuwa tuni an dora ta a kan magunguna, kuma ana ba ta kulawar da ta dace a wurin da aka kebe ta.

Ya kuma ce za a fara aikin feshin magungunan kashe beraye da makamantansu a daukacin yankin ranar Alhamis.

Ga dai yadda hirar kwamishinan ta kasance da BBC:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hira da kwamishinan lafiya na Borno kan zazzabin Lassa

Cutar zazzabin Lassa dai ta samo asali ne daga garin Lassa na karamar hukumar Askira Uba a jihar Bornon, lokacin da wasu bakin turawa suka fara kamuwa da ita shekara sama da arba'in da suka gabata.

Labarai masu alaka