Giwaye sun fi kowacce dabba mai shayarwa kwanan tsaye

Giwaayen na barcin sa'oi biyu ne kacal
Image caption Giwaye sun fi kowacce dabba karancin barci a cewar wasu masana kimiyya

Wasu masana kimiyya da suka bibiyi rayuwar wasu giwaye guda biyu a ƙasar Botswana sun gano cewa giwayen sun fi kowacce irin dabba mai shayarwa a banƙasa ƙarancin barci.

Giwayen dai na barcin sa'a biyu ne kacal, akasari kuma da daddare.

Idan suna tsare, giwayen kan yi barci ne na tsawon sa'a uku ko hudu a rana.Farfesa Paul Manger na jami'ar Wits ya ce binciken ya zo da bazata

"giwayen da aka yi nazari a tsare, an gano suna kwanciya a mafi yawan lokuta kuma suna yin barcin sama da tsawon sa'a uku ko hudu, sai dai idan suka shiga daji akasarin barcinsu a tsaye suke yi."

Giwayen waɗanda mata ne a cikin garke, wasu lokuta sukan shafe tsawon kwanaki ba su rintsa ba, sai dai su riƙa ƙyaƙƙyafta ido ko magagi a duk bayan kwana uku ko huɗu.

Babu wata masaniya kan dalilin da ya sa giwa wadda aka san ta da kaifin tunani, take iya rayuwa da gyangyaɗi duk da yake barci na da wani muhimmin matsayi a fagen tunani.