Kocin Barcelona zai ajiye aiki a karshen kakar bana

Luis Enrique, Kocin Barclona Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Luis Enrique ya ce zai ajiye aiki a matsayinsa na babban kocin Barcelona don ya huta

Babban kocin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Luis Enrique ya ba da sanarwar cewa zai ajiye aiki a ƙarshen kakar bana.

Enrique zai shafe tsawon kakar wasa uku kenan a ƙungiyar.

A shekararsa ta farko ya ɗauko wa Barcelona kofin zakarun Turai, kuma ya jagorance ta lashe gasar La Liga karo na biyu a bara.

Sai dai duk da kasancewar Barcelona a saman teburin La Liga, ƙiris ya rage a koro ta daga gasar Zakarun Turai ta bana bayan Paris St-Germain ta yi mata raga-raga da ci huɗu da nema.

Luis Enrique ya ce babban dalilinsa na barin aiki shi ne buƙatar hutu.