Za a kafa asusun goyon bayan zubar da ciki

Lilianne Ploumen Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Holland za ta taimakawa masu son zabar da ciki

Ana gudanar da wani taro a Belgium, domin neman tallafin kudi ga kungiyoyin da ke goyon bayan zubar da ciki.

An kira taron ne domin daukar mataki a kan shawarar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yanke, cewa gwamnatinsa za ta dakatar da bayar da kudade ga kasashe masu tasowa domin gudanar da ayyukan da suka shafi zubar da ciki.

Mahalarta taron sun hada da wakilai daga kasashe 50, da hukumomin da ba na gwamnati ba, da kuma kamfanoni masu zaman kansu.

Wata ministar gwamnatin Holland, Lilianne Ploumen, ta ce kamata ya yi a bai wa mata damar zabin abin da suke son yi da jikinsu.

Sanarwar dakatar da bayar da kudaden tallafin da Amurka ta fitar a watan Fabrairu, ita ce ta fi yin tasiri fiye da duk wani takunkumi da Washington ta taba sanya wa kungiyoyin da ba na gwamnati ba, da suka hada da masu samar da bayanai game da zubar da ciki.

Sai dai ana ganin matakin Mista Trump din zai sanya ayyukan da suka shafi lafiyar mata masu haihuwa da kungiyoyin masu cutar HIV/AIDS.

Labarai masu alaka