Dakarun Syria sun sake kwato birnin Palmyra daga hannun IS

Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Syria sun fatattaki mayakan IS daga Palmyra

Dakarun kasar Syria da masu mara musu baya na kasar Rasha sun ce sun sake kwato daukacin birnin Palmyra daga hannun kungiyar IS.

An ba da rahoton cewa dakarun sun kutsa can cikin birnin na Palmyra--bayan da mayakan IS suka fice.

A karon farko da suka shiga birnin mayakan ISIS sun fara da lalata gine-ginen tarihin da ake ji da su.

A watan Mayun shekarar da ta gabata ne aka fatattaki 'yan ISIS din amma suka sake kwace birnin da kewayensa a cikin watan Disamba.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Russia ta ce dakarun Syria sun samu nasara tare da goyon bayan dakarunta na sama

Jakadan kasar Syria a Majalisar Dinkin Duniya Bashar al-Jaafari ya tabbatar da sake kwace birnin a ranar Alhamis.

Ya ce ''an kwace birnin daga hannun kungiyar 'yan ta'adda'', kana shugaba Bashar al-Assad ya cika alkawarinsa na fatattakarsu.

Kasar Rasha ta ce dakarun Syrian sun samu galabar kwace Palmyra da taimakon kai hare-hare ta saman da ta yi.

A kasar ta Russia, kafofin yada labarai sun ba da rahoton ministan tsaro Sergei Shoigu na shaidawa shugaba Vladimir Putin cewa dakarun Syria da taimakon sojojin saman Russsia sun kwace daukacin birnin Palmyra.

Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil'adama a kasar ta Syria da ke Birtaniya ta ce an yi bata kashi da lugudan wuta a kan birnin mai dimbin tarihi tun daga ranar Laraba.

Ta kuma ce masu tada kayar bayan sun dasa nakiyoyi a wurare da dama kafin su fice.