Ƙayatattun hotunan Afirka: 24 Fabrairu zuwa 2 Maris 2017

Ivorian Naky Sy Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata jarumar fina-finai daga Ivory Coast, Naky Sy Savane a Ouagadougou babban birnin kasar Burkina Faso yayin bikin nunin fina-finan Afirka na bana
Masu dafa abinci a Ouagadougou, Burkina Faso Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban mutane ne suka hallara a Ouagadougou domin bikin baje-kolin fina-finan Afirka, kasuwa ta buɗe ga 'yan kasuwa kamar masu dafa abinci
Shugaba Robert Mugabe Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wani ɓangare na bikin cikar shugaban ƙasar Zimbabwe, Robert Mugabe shekara 93 da haihuwa.
Shugaba Robert Mugabe Hakkin mallakar hoto AP/REUTERS
Image caption Mista Mugabe ya caɓa ado da wata hular malafa ta musammam mai ɗauke da tambariin sa-hannunsa da kuma shekarar da aka haife shi ta 1924 a ɗaya gefen
Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu yaran Sudan ta Kudu a sansanin 'yan gudun hijira na Palorinya da ke Uganda
Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Layin 'yan gudun hijira a wata cibiyar karɓar abinci ta majalisar dinkin duniya da ke Kuluba. Majalisar Dinkin Duniya ta ce 'yan gudun hijirar miliyan 1.5 na Sudan ta kudu ke zaune a Uganda tun a watan Disamban 2013 bayan ɓarkewar yaƙi
Addis Ababa, Ethiopia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani mayaƙi ɗan kasar Habasha rike da takobinsa a wani biki da aka yi cikin birnin Addis Ababa domin murnar cika shekara 121 da yaƙin Adwa
Sojojin Ethiopia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojojin Habasha sun yi nasara a kan 'yan Italiya a wani yaƙin da suka gwabza a kusa da wani gari da ke Arewacin Adwa a shekarar 1896.
Algeria Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Jaruman fina-finan Algeriya sun yi shiga irinta ta ashana mai jan kai lokacin da suke wasa da ake kira Torchaka, na Ahmed Rezza a babban birnin Algiers, ranar juma'a
Artistes performing at a cultural festival in Bingerville, Ivory Coast - Saturday 25 February 2017 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Fasihai suna wasa yayin wani bikin nuna al'adu a Bingerville, wani gari da ke kudu maso gabashin Ivory Coast…
Ivory Coast Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Bikin Ivoiro-Antillais domin tabbatar da zumunci tsakanin Ivory Coast da Caribbean
Bikin Ivoiro-Antillais a Ivory Coast Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mawaka na raye-raye da wasu nau'o'in kayan kiɗan gargagiya a bikin Ivoiro-Antillais
Djiboutian, Faransa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan ƙasar Djibouti a Faransa suna zanga-zanga a birnin Paris don nuna adawa da ziyarar da shugaba Ismail Omar Guelleh yake shirin kai wa, bayan ya lashe zabe karo na hudu
Santiago daga Chile Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wani mai tallata shigar tufafi a wani bikin baje-kolin tufafin Afirka a Santiago babban birnin ƙasar Chile, da wata ƙungiyar 'yan Afirka mazauna Chile ta shirya.
Maiduguri ,Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani mutum da iyalinsa na hutawa a karkashin wata babbar mota a birnin Maiduguri da ke Arewa maso Gabashin Nijeriya
Afirka ta Kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sandan Afirka ta Kudu sun kai samame a wani gida na wani mutum da ake jin mai dillancin ƙwaya ne a birnin Pretoria
Afirka ta Kudu Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wani maci kenan don nuna adawa da 'yan ci-rani a birnin Pretoria. Nan wani ɗan ƙasar waje ne yake yi wa masu zanga-zangar nuni yayin da 'yan sanda suka shiga tsakani
Afrika ta Kuda,Pretoria Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'yan Afrika ta kudu masu zanga-zanga karmar wannan suna zargi 'yan ci-rani da kwace musu ayyuka, kuma suna zarginsu da shiga ƙungiyoyin karuwanci da safarar miyagun ƙwayoyi
A man riding a horse in a dam in Greyton, South Africa - Saturday 25 February 2017 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A ranar Asabar, wani mutu da dokinsa suna ninƙaya a wata madatsar ruwa cikin Greyton, na lardin Overberg da ke kudu maso yammacin Afirka ta kudu, kusa da tsaunukan Sonderend.

Image courtesy of AP, AFP, EPA, Getty Images, Reuters

Labarai masu alaka